Sakamakon gwajin da hukumar NCDC ta yi wa gwamnan Jihar Bauchi Bala Mohammed, na coronavirus, ya nuna cewa gwamna Bala na dauke da cutar.
Sai dai kuma Iyalan sa shida da aka dauki jinin su duk sun nuna basu dauke da cutar.
Yanzu dai gwamna Bala ya killace kansa sannan likitocin sa sun isa wurinsa tare da jami’an hukumar NCDC.
Gwamna Bala ya roki makarraban sa da sauran ma’aikata da suka yi hudda da shi cewa su gaggauta zuwa a duba su sannan su killace kan su.
Gwamna bala ne jami’ain gwamnati na biyu da ya kamu da cutar a Najeriya zuwa yanzu.
Idan ba a manta ba, shugaban Ma’aikatan fadar shugaban kasa shima na killace bayan an tabbatar da ya kamu da cutar.
Discussion about this post