GARKUWA DA MUTANE: ‘Yan sanda sun ceto dalibai ‘yan bautan kasa 4 a Zamfara

0

Runduna ‘yan sandan jihar Katsina tare da hadin guiwar wasu tubabbun mahara a jihar Zamfara sun ceto wasu masu bautan kasa hudu da wani mutum daya daga masu garkuwa da mutane.

Kakakin ‘yan sandan jihar Katsina Isah Gambo ya sanar da haka da yake hira da manema labarai ranar Alhamis.

Gambo ya ce an yi garkuwa da wadannan mutane ranar 9 ga watan Maris sannan aka ceto su ranar 11 ga wannan wata.

Ya ce ‘Yan bautan kasar sun kamo hanyar zuwa sasanin horas da su dake jihar Zamfara ne a nan masu garkuwa da mutane suka kama su tsakanin Funtua zuwa Gusau.

Gambo ya ce sun yi nasaran ceto wadannan mutane ne a dalilin hadin kai da wasu tubabbun mahara suka basu inda suka nuna musu maboyar masu garkuwa da mutane a wannan yanki.

“Tubabbun maharan sun san kowani tudu da kwari dake dajin Zamfara. Mun iske mutane shida a wannan wuri amma duk mun harbe su duka sannan muka ceto Oladehin Paul, Ojo Temitope, Ojewale Elizabeth da Adenigbuyan Adegboyega

“Mun kuma kwato bindigogi uku, a ciki a kwai babban bindiga kiran AK 47’’.

Idan ba a manta ba a wannan mako ne Rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa ita ma ta kama masu garkuwa da mutane,fyade da ‘yan fashi da makami 71 a bangarori daban daban a jihar.

11 daga cikin mutanen da rundunar ta kama sun yi saranda a gaban kungiyar Miyetti Allah wanda kungiyar ta damka su a hannun jami’an tsaro.

Share.

game da Author