Firaye Ministan kasar Birtaniya Boris Johnson, ya Kamu da Coronavirus

0

Firaye ministan kasar coronavirus Boris Johnson ya kamu da cutar coronavirus.

Johnson ne shugaban kasa na farko a duniya da aka tabbatar ya kamu da cutar.

Tuni dai har ya killace kan sa domin gudun kada ya harba wa wasu.

Kasar Birtaniya na daga cikin kasashen da cutar ta yi wa haan kawara.

Mutane da dama sun kamu da cutar a kasar.

A kasar Spaniya ma abin sai kara gaba-gaba yake yi, inda ya zarce kasar Italiya da kullum ake samun daruruwan mrane da suke kamuwa da cutar.

A kasar Spaniya, an samu mutane sama da 500 da suka mutu a cikin kwana daya.

Haka ita ma kasar Amurka, yanzu ta zarce hatta kasar chana da nan ne cutar ta fara bullowa.

Bayan haka, a ranar Juma’ a shugaban kasar Amurka ya roki likitocin da ke kaunar zuwa kasar su garzayo maza-maza su shigo kasar domin yin aiki.

Gwamnatin Amurka ta ba da umarnin a amince wa ma’aikatan asibiti a ofisoshin jakadun kasar dake kasashen duniya su shigo kasar domin a basu aikin yi.

Ko da ko kasar da Amurka ta taba haramta wa ‘yan kasan shigowa ne.

A Najeriya kuwa, kusan duka jihohin kasar sun garkame jihohin su.

Hatta ayyukan ibada da ya hada da yin sallan juma’a da salloli biyar a masallaci duk an dakatar.

Zuwa yanzu dai akwai akalla mutane 65 da aka tabbatar sun kamu da cutar, sannan an samu rasuwar mutum daya, mutum biyu kuma sun warke.

Share.

game da Author