Fellaini, Dybala, Maldini, Matuidi, sun kamu da coronavirus

0

Tsohon dan kwallon Manchester United dake kasar Birtaniya, Marouane Fellaini ya shiga cikin jerin ‘yan wasan Kwallon kafan da suka kamu da cutar coronavirus.

A sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter, Fellaini ya ce ya kamu da citar coronavirus, kuma yana sa ran zai ci gaba da wasa da zaran ya warke.

Dan wasan na buga kwallo a kasar Chana ne yanzu. Sai dai yanzu haka yana kwance a asibiti inda aka killace shi.

Sanarwar da kungiyar kwlon kafan da Fellaini ke wasa ta fitar ta ce “Gwajin da aka yi ya tabbatar da cewa dan wasansu Fellaini ya kamu da cutar.”

Haka nan shima dan wasan kwallon kafan Juventus, Dybala ya ce shi da buduwarsa Oriana sun kamu da cutar.

“Ni da Oriana muna da cutar, amma muna cikin yanayi me kyau”

Haka kuma fitaccen tsohon dan wasan AC Milan da kasar Italiya, Paolo Maldini ya kamu da cutar coronavirus.

Dan wasa Dybala ne dan kwallon mungiyar Juventus na uku da aka tabbatar ya kamu da Coronavirus bayan dan wasan baya Daniele Rugani da kuma Blaise Matuidi da suma duk sun kamu da cutar.

Share.

game da Author