Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan, ya bayyana rashin jin dadin yadda ya ga Cibiyar Killace Masu Cutar Coronavirus a Abuja.
Yayin da ya samu cibiyar a cikin halin ko in kula, ya kuma cika da mamaki ganin yadda ya ga cibiyar ashe daki daya ne tal, kuma ba a kamo hanyar kammalawa ba.
Dalili kenan ya yi tambaya a cikin fushi ya ce me ya sa ba za a kira daki daya cibiyar killacewar ba, “duk kuwa da bimbin kudi har naira milyan 600 da aka ware wa cibiyoyin domin daukar masu dauke da cutar.”
Lawan ya nuna wannan damuwar ce a lokacin da ya ziyarci cibiyar killace masu dauke da cutar coronavirus a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abuja, da ke Gwagwalada.
“Wannan cibiya dai suna ce kawai, kuma bai ma dace a ce a nan ne za a killace masu cutar Coronavirus ba. Saboda ba a ma gama ba ballantana a ce a kammala ranar Alhamis.” Inji Lawan.
“A yanzu fa mu na cikin halin gunadar da ayyukan gaggawa. Don babu mai cutar a halin yanzu da za a kawo a killace, kada wannan dalili ya sa a ki maida hankali wajen karasa aiki da wuri. Ya kamata a yi duk abin da za a yi, domin a kowane lokaci za a iya samun wanda ya kamu da cutar.”
A na su bangaren, jami’an Cibiyar Kula da Cututtuka ta Kasa sun bayyana na Shugaban Majalisar Dattawa cewa har yanzu gwamnati ba ta sakar musu kudi ba daga waccan naira milyan 620 da ta ce ta kebe domin aikin hana yaduwa da kamuwa da Coronavirus.
Jin haka sai Lawan ya yi kira ga Ma’aikatar Kudi ta Tarayya da ta gaggauta sakar musu da kudaden.
Ya kuma ce Majalisar Dattawa za ta tabbatar da cewa an saki kudin da gaggawa.