El-Rufai ya nada tsohon Sarkin Kano Sanusi shugaban gudanarwar Jami’ar jihar Kaduna

0

Awowi bayan nada shi mataimakin hukumar bunkasa tattalin Arziki da saka jari ta jihar Kaduna Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya sake nada tsohon Sarkin Kano Muhammadu Sanusi shugaban kwamitin gudanarwar Jami’ar Jihar Kaduna, KASU.

Kakakin gwamnan jihar, Muyiwa Adekeye ya sanar da haka a takarda da ya raba wa manema labarai ranar Laraba.

El-Rufai ya ce yayi haka ne domin daukaka martabar jami’ar a idanun duniya ganin cewa Sanusi mutum ne dake da kwarewa, dattaku da kima a idanun manyan kasasshen Duniya.

Ya ce nada shi zai kawo wa wannan jami’a martaba a wannan lokaci da gwamnati ta kara bunkasa makarantar da gyara ta domin ci gaban mutanen jihar da kasa baki daya.

El-Rufai ya gode wa shugbana gudanarwan jami’ar wanda ya sauka da shine shugaban ta na farko tun da aka kafa jami’ar. Mai Tagwai Sambo.

Idan ba a manta ba, Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya nada tsohon sarkin Kano Muhammadu Sanusi mataimakin shugaban hukumar KADIPA, dake da hakkin kula da hannaye jari da bunkasa tattalin arzikin jihar.

A sanarwan da Kakakin gwamna El-Rufai, Muyiwa Adekeye, ya fitar ranar Talata, El-Rufai ya ce gwamnati ta zabo kwararru a harkar sanin tattalin arziki da saka jari kafin ta sanar da mambobin wannan hukuma.

Mataimakiyar gwamnan jihar Kaduna, Hadiza Balarabe ce zata shugabanci wannan Hukuma, shi kuma tsohon sarki Sanusi a matsayin mataimakin wannan hukuma.

Haka kuma, tsohon gwamnan jihar Kano Rabiu Kwankwaso ya yi tir da tsige sarki Sanusi da Ganduje yayi, yana mai cewa wannan shiri ne daga fadar Shugaban kasa.

Kwankwaso ya ce shugaba Muhammadu Buhari ya san da maganar tsige sarki Sanusi kuma yana da hannu a ciki.

Share.

game da Author