Gwamnatin Jihar Kaduna ta kafa dokar-ta-baci, kenan an hana kowa fita aiki, kasuwanci ko wata hada-hada in banda jami’an tsaro da jami’an kula da lafiya ko wasu masu wasu ayyukan musamman.
Mataimakiyar Gwamna, Hadiza Balarabe ce ta yi wannan sanarwa, a ranar Alhamis, tare da cewa kafa dokar ta zama dole, saboda jama’a sun bijire wa umarnin da gwamnati ta bayar na matakan da ya kamata a dauka domin hana cutar Coronavirus bulla da watsuwa a jihar Kaduna.
Ta ce kwamitin aiki kan dakile Coronavirus ya sake zama a yau Alhamis, inda ya fahimci cewa masu babura da motocin haya da sauran wadanda aka hana zirga-zirga, duk sun ki bin umarnin da aka yi tun da farko.
A kan haka ne Hadiza ta ce gwamnati ta lura ba ta da wata mafita sai kawai a saka dokar walwala, wadda za ta tilasta wa kowa zaman gida, a iarkashin dokar Najeriya ta 1999.
“Daga 12 na daren Alhamis, an haramta duk wasu taruka na bukukuwa ko gidajen shakatawa.
” Dukkan wuraren taruka ko wuraren ibadar da suka karya wannan doka, to za a kwace hakkin mallakar wuraren daga gare su, sannan kuma a rusa wuraren.” Inji sanarwar.
Hadiza ta ce daukar wadannan tsauraran matakai ya zama dole, saboda gwamnati ba ta da isassun kudade da ciniyoyin kula da marasa lafiya, idan har aka yi sakacin da aka bari har cutar ta bulla a Kaduna
Dangane da zirga-zirga kuwa, an hana zirga-zirgar ababen hawa a cikin Kaduna, amma matafiya masu wucewa, an yarda su bi ta hanyar kewaye wa ciki n gari, wato by-pass.
Hadiza ta gode wa gwamnatin tarayya da ta bi shawarar jihar Kaduna, ta dakatar da zirga-zirgar jiragen kasa, har zuwa lokacin da za a rabu da annobar Coronavirus.
Ta kuma gode wa malaman addinai da suka taimaka wajen wayar da kan mutane.
Ta ce duk wanda ya karya doka, za a kama shi, sannan a hukunta shi.