Yayin da wasu manyan masu sharhin kwallo na duniya ke ganin cewa wasan El-Clasico da aka buga Lahadi tsakanin Real Madrid da Barcelona bai yi armashi sosai ba, wasu kuwa na ganin cewa wasan ya burge sosai.
Barcelona ta sha kashi da ci 2:0 a filin wasan Santiago Barnabeu, a birnin Madrid. An tafi hutun rabin lokaci inda Barcelona ta yi rashin sa’ar jefa kwallaye a ragar Madrid. Wannan ya bai wa ‘yan wasan ta haushi matuka.
Madrid ts rike wuta bayan dawowa daga hutun rabin lokaci, inda suka rika yin halin da suka saba, kuma suka kware, wato maida kai hari nan da nan, da a Turance a ke kira ‘counter attack.’
Vinicious Junior na Madrid ya karya lagon Barcelona a daidai minti na 72, inda ya ja kwallo ta gefen hagu, ya shiga cikin gidan Barcelona ya ci kwallo, bayan ya buga ta taba kafar dan baya, Gerrard Pique.
Tarihi: Vinicious ya karya tarihin da Messi ya kafa a matsayin sa na dan wasa mafi kankantar shekaru da ya taba cin kwallo a wasan El-Clasico.
Messi ya fara cin Madrid ya na da shekaru 20, yayin da Vinicious ya saka kwallo a ragar Barcelona a ranar Lahadi ya na da shekaru 19 da kwanaki 236 a duniya.
Mariano Diaz: Ya ajiye tarihi shi ma inda ya ci kwallo ta biyu a farkon taba kwallon sa, bayan ya shigo wasan daga baya, an kusa tashi daidai minti na 92.
Karim Benzama shi ma ya kafa tarihi ta ranar, inda ya buga wasa na 500 cif a Real Madrid.
Messi da Benzama ba su tabuka wasa kamar yadda aka yi tunani, yakini ko zaton za su yi ba. Watakila shi ya sa wasu ke ganin wasan bai yi armashin yadda aka so ya yi ba.
Ronaldo A Cikin ‘Yan Kallo: Kallo ya koma sama, a lokacin da aka tsinkayi tsohon Dan wasan Madrid, wanda ya koma Juventus, Christian Ronaldo a sahun layin fitattun manyan bakin ‘yan kallo.
Ronaldo ya je kallon gurugubjin wasan El-Clasico ne daga Turin, birnin Italy, bayan an dage wasan Juventus da Inter Milan saboda barazanar cutar Coronavirus da ta fantsama a Italy.
Hakan ya sa Ronaldo ya je kallon wasan, kuma ya rika zuga ‘yan wasan Madrid domin su yi nasara a kan Barcelona.
An nuno shi ya na murna, a lokacin da Vinicious ya fara jefa kwallo a ragar Barcelona. Shi kuma ya ruga gefen fili, ya yi irin tsallen murnar da Ronaldo ke yi idan ya yi kwallo.
A shekaru tara da Ronaldo ya shafe a Real Madrid, ya buga El-Clasico sau 30.
Cacar-Bakin Pique Da Ramos: Bayan kammala wasan, Gerrard Pique ya yi hira da ‘yan jarida ya ce bai taba buga El-Clasicon da Madrid suka buga wasan ‘yan dagaji ba, kamar yadda Madrid ta buga wasan rabin lokaci na farko.
Ya ce harbar-Mati suka rika yi, kuma ya yi takaicin rashin jefa musu kwallaye a farkon rabin lokacin da Barcelona ba ta yi ba.
A na sa martanin, Ramos ya ce ai na wanda ke daukar sabbatun Pique da muhimmanci. Su ma ‘yan jarida na bugawa ne kawai don su ci kasuwa da kanun labarai kawai.
Ya ce borin-kunya ne ya ke yi, kuma ba zai iya kankare nasarar da Madrid ta yi a duniya ba.
A karshe ya ce, “da irin ‘yan wasan da suka san abin da suke yi ne, kamar Andrea Iniesta ya fadi maganar, sai Madrid ta ji haushi. Amma irin su Pique wa ya damu da shi? Wa kuma ya dauki zantukan sa ba kwarai? Duk bulkara ce kawai ya ke yi.
Ramos ya fi kowa samun jan kati a tarihin Madrid. Shi kuma Gerrard Pique ya fi kowa cin gidan su da kan sa a tarihin Barcelona.
Discussion about this post