Dan kasar Gabon ya Kamu da Coronavirus

0

Ministan yada labarai kasar Gabon Edgard Miyakou ya sanar cewa an gano cutar Coronavirus a jikin mutum daya a kasar.

Miyakou yace gwamnati ta samu tabbacin bullowar cutar ne a daren Alhamis a jikin wani dan kasar mai shekaru 27 da ya shigo kasar bayan ya dade da zama a Bordeau kasar Faransa.

Ya ce tuni an killace wannan mutum a asibiti inda har ya fara samun sauki.

Kasar Gabon itace kasa ta 10 kenan a kasashen dake Kudu da Saharan Afrika da wannan cuta ke bullowa.

GHANA

Ministan lafiyar kasar Ghana Kwasi Agyemang-Manu ya sanar cewa mutane biyu sun kamu da Coronovirus a kasar.

Kwasi yace an gono haka ne ranar Alhamis bayan gwajin cutar da aka yi wa mutane 57 da suka shigo kasar.

“Sakamakon gwajin ya nuna cewa mutane biyu ‘yan kasar Ghana da suka dawo daga kasashen Norway da Turkey na dauke da cutar.

Ya ce an killace wadannan mutane a asibiti sannan har an fara gudanar da bincike domin gano mutanen da ka iya kamuwa da cutar a wajen mu’amula da wadannan mutane.

Kwasi ya ce gwamnati za ta hada hannu da hukumomin fannin kiwon lafiyar kasar domin hana yaduwar cutar.

Bayan haka a ranar Laraba shugaban kasar Nana Addo Dankwa Akufo-Addo ya yi kira ga mutanen kasar da su kwantar da hankalinsu cewa gwamnati ta dauki tsauraren matakan hana yaduwar cutar.

Akufo-Addo yace gwamnati ta ware dala miliyan 100 domin kafa matakan hana yaduwar cutar koda cutar ta barke a kasar.

A yanzu dai coronavirus ta bullo a kasashen Afrika 15 inda akalla mutane sama da 100 sun kamu da cutar.

Kasar Masar ce kasar da ta fi fama da cutar a Nahiyar Afrika.

A cikin wannan mako kuma kungiyar kiwon lafiya ta duniya (WHO) ta sanar cewa Coronavirus ta zama annoba a duniya.

Share.

game da Author