DALLA-DALLA: Yadda #Coronavirus ta kashe mutum sama da 3,000 a duniya

0

3,000: Cutar Coronavirus wadda ta fara barkewa da bulla a kasar China, zuwa yanzu ta kashe mutane sama da 3,000 a cikin kasar da sauran kasashe duniya 50 da cutar ta bulla.

90,000: Adadin wadanda suka kamu a Chana da sauran kasashen duniya 50, ya zarta mutum 90,000, kamar yadda Hukumar Lafiya ta Duniya ta bayyana a safiyar Litinin.

Daurin Kamuwa: Cikin makonni biyu, a China ana samun raguwar fantsamar cutar, yayin da a sauran kasashen duniya ta ke kara fantsama kamar gobarar-daji.

Nahiyar Asiya: Nan ne yankin da cutar ta fi fantsama banda kasar China. Amma an sake bada rahoton mutuwar mutum 42 a China a safiyar Litinin.

Kasashe 25: WHO ta ce kasashen da suka kamu da cutar guda 25, duk matafiya ne suka dauko cutar daga wasu kasashe suka shigar musu da ita.

Kasashe 3: Kasashen Iran, Italy da Koriya ta Kudu ne aka fi samun yawan masu dauke da cutar baya ga kasar China.

Mutum 4,212: Wadannan su ne adadin mutanen da suka kamu da cutar a kasar Koriya ta Kudu.

Jinjiri: An samu jinjiri mai kwanaki 45 a duniya dauke da cutar a kasar Koriya ta Kudu. Kuma shi ne mafi kankantar shekaru a aka samu ya kamu da Coronavirus a duniya.

Mutane 26: Shi ne adadin mutanen da cutar ta kashe a Koriya ta Kudu. Can ne kuma ta fi yin kisa a kasashen da ke da kusanci da China.

Mutane 50: Su ne adadin mutanen da cutar ta kashe a kasar Iran. Kuma ta yadu sosai a kasar, bayan ta ci ran manyan jami’an gwamnati da na sauran jama’a.

Mutane 30: Ta kashe mutane sama da 30 a kasar Italy. An kuma bada rahoton cewa an kai cutar kasashe daga Italy, ciki kuwa har da Najeriya.

Mutane 89: Adadin wadanda killace a Amurka, cikin su kuwa har da wasu sama da 30 da aka killace bayan an sauke su daga jirgin ruwan da aka samu fasinjoji da dama dauke da cutar.

Kowa Ya Kwana Da Shiri: Shugaban Hukumar Lafiya ta duniya (WHO), Tedros Ghebreyesus ya ce kada ma wata kasa ta yi tunanin cewa wannan cuts ta Coronavirus ba za ta shafe ta ba.

Ya ce cutar ta rigaya ta zama babbar annoba a duniya. Don haka a tashi tsaye a ci gaba da neman dakile ta kawai.

Share.

game da Author