Shugabar Hukumar Kula da Tashoshin Ruwa ta Kasa (NPA), Hadiza Bala Usman, ta karyarta zargin da ake yi cewa wai tana da alaka ta kud-da-kud da Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai.
Hadiza ta kuma karyata cewa wai kusantar ta da El-Rufai ne ya sa aka ba ta mukamin shugabancin NPA cikin 2016.
Shugabar ta NPA wadda ita ce Shugabar Ma’aikatan Gwamna Nasir tsakanin 2015 zuwa 2016, ta karyata wadannan zarge-zargen a wata tattanawar musamman da gidan talbijin na TVC ya yi da ita a ranar Litinin.
Sun yi hirar ce da ita domin tunawa da zagayowar Ranar Mata ta Duniya.
Ta bayyana surutan da ake yi mata cewa wai El-Rufai saurayin ta ne a matsayin dadadden labarin da aka dade ana gulma da yamadidi ta a kai tun da dadewa.
“Ni ba budurwar sa ba ce, domin ni gwamnan ubangina ne, kuma oga na. Ya taimaka min sosai wajen ciyar da ni gaba a ayyuka, kamar yadda ya rika yi wa dukkan matan da suka yi aiki a karkashin sa.
“Kamar yadda ka sani ai jihar Kaduna ce jiha ta farko daga Arewa da aka fara yin mataimakiyar gwamna. Don haka kun ga shi ya na da wannan kokari na ganin mata sun kai matakai ko manyan matsayi a kasar nan.
“Saboda haka maganar ni farkar sa ce, duk kaya ce babu kamshin gaskiya ko kadan.” Inji Hadiza.
Hadiza mai shekaru 44 a duniya, ‘yar siyasa ce, kuma ‘yar rajin kare hakkin mata ta kungiyar #Bringbackourgirls.
An nada ta shugabancin NPA cikin Yuli, 2016. Hakan kuwa ya janyo tsegumi da ka-ce-na-ce da gulmace-gulmace kan Shugaba Muhammadu Buhari.
An rika zargin cewa ba ta da wani ilmi ko kwarewar da za ta shugabanci NPA.
Ta ce surutan da ake yi a kan ta duk kokari ne domin ya kwashe kafafun mata, a kayar da su domin kashe musu guyawun samun manyan matsayi a Najeriya.
Da ta ke kare Buhari a zargin da ake masa cewa ya na nuna kabilanci a nada manyan mukamai inda yak e fifita ‘yan Arewa, sai ta ce ba haka ba ne.
“in dai ka yi aikin da aka ce ka yi, to kada ma wasu surutai su dame ka. Domin karairayi ne kawai.”