Dalilin da ya na ziyarci abokina Sanusi, kuma muka tashi zuwa Ikko – El-Rufai

0

Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya bayyana cewa hukuncin kotu ta bashi daman ya ziyarci garin Awe in da ake ajiye da abokin sa domin ya ga halin da yake ciki.

” Kotu ta ba mai martaba daman zuwa ko ina, ban ga dalilin da zai sa kuma wai a hana wani ziyartar sa ko kuma hana shi watayawa ba.

” Mu a jihar Kaduna muna daraja sarakunan mu matuka, saboda haka duk inda muka iske mutane masu daraja haka zamu girmama su.

Bayan awa hudu da El-Rufai yayi a garin Awe tare da Sanusi, batan sallar juma’a sai kuma suka dunguma tare da mahaifiyarsa da ‘ya’yan sa biyu zuwa filin jirgin Abuja domin tashi zuwa Ikko, jihar Legas.

Mutanen garin Awe sun yaba da zaman Sanusi a wannan gari na Awe, san kuma yi masa fatan Alkhairi Sun bashi dama ya ja su sallan Juma’a a garin.

Dauda Muhammad-Awa ya ce ” ban ji dadi ba da aka tsige shi daga sarautan Kano sai dai nayi kuma matukar farincikin zaman sa a wannan gari na Awe.

” Mu a wannan gari muna cikin farin iki domin zaman sarki Sanusi a wannan gari rahama ce a gare mu. Saboda kunga yanzu ai garin Awe ya karade ko ina a shafukan jaridu da duniya.

Dauda Ibrahim cewa yayi zuwan Sanusi garin Awe ya sa sun samu karin tsaro a garin. Sai dai yana kira ga gwamnati da ta gyara musu hanyoyoyi.

Ita kuwa Fatima Kande, cewa tayi mutanen Awe za su tabbata sun dadada wa tsohon sarki Sanusi rai da ba zai taba mantawa da zaman sa a wannan gari ba. Wanda ko da ya gama zaman zai rika dawowa yana ganin su akai-akai.

Share.

game da Author