Tsohon shugaban Kasa kuma shugaban kwamitin sasanta tsohon Sarkin Kano Sanusi da Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Ganduje, Abdussalami Abubakar ya bayyana cewa lallai da a ce Buhari ya duba shawarwarin da suka bada a rahoton su da yana ganin ba zai kai ga tsige sarki Sanusi ba.
Abdussalami Abubakar ya amsa tambayoyi ne a hira da yayi da muryar Amurka.
” Babban abinda ya bani mamaki shine yadda abin ya kai ga har an tsige sarki Sanusi.
” Lallai mun zauna da Sarki Sanusi da bam kuma munji daga garesa, sannan mun zauna da Gwamna Abdullahi Ganduje, shima mun tattauna da shi matuka. Bayan haka mun bar su tare sun zauna sun tattauna kafinnan muka rubuta sakamakon ganawar mu da su.
” Abin da muka ji sannan muka gani, ban yi tunanin har zai kai ga wannan matsayi da muak shiga yanzu ba. Bayan mun Kammala zaman mu da su mun daidai ta komai sannan muka mika wa shugaban Kasa Buhari sakamakon binciken mu kai tsaye.
” Ba zan iya cewa ko Buhari ya karanta wannan rahoton binciken ba ko kuma A’a. Abin da zai daure min kai shine zai yi wuya a ce ya gani kuma ya karanta sannan ace wai har an kai ga haka. Zan yi matukar mamaki a kai. Abin da kawai bai yi min dadi ba shine duk wahalar da muka yi na ganin mun warware matsalar ya zama a banza yanzo.
Idan ba a manta ba ko tsohon gwamnan Kano Rabiu Kwankwaso ya bayyana cewa Buhari na da hannu dumu-dumu a tsige sarkin Kano Sanusi.
Haka kuma mutanenn Najeriya da dama sun koka kan yadda wannan matsala ya kai ga sai da aka tsige shi daga sarautar Kano.