Labarin bulluwar cutar covid-19 a duniya ta fara ne a karshen shekarar 2019 a yankin Wuhan na kasar China.
Daga nan ne cutar ta fara yaduwa zuwa sassan kasashen duniya da suka hada Italiya, Spaniya, Amurka, Iran da sauransu. kuma rohotanni na cigaba da nuni cewa ana ta kamuwa da kuma rasa rayuka ciki harda kasashen Afirika.
A watan Fabrairu ne cutar ta fara shigowa nahiyar Afrika ta hanyar wasu yan kasashen waje da ke ci rani a yankin Afirika.
Kamar a kasar mu ta Najeriya, wani dan Italiya da ke aiki a jihar Ogun ne ya shigo da cutar bayan ya dawo daga gida Milan. A halin yanzu dai, ya warke sai dai ansamu wasu da ke dauke da cutar ciki kuma har da wasu manyan jami’an gwamnatin Tarayyar Najeriya da suka dawo daga kasashe masu fama da wannan cutar,ciki harda da shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, wato mallam Abba Kyari da gwamnan jihar Bauchi Bala Muhammad da sauransu.
Kamar yadda aka yi ta sanarwa daga jihohi cewa, ansa dokokin kare kai da suka had a da rufe makarantu da tsaftace hannu da sauransu. Wasu jama’a a jihar Kaduna sun ta cece kuce Kan a rufe makarantu, amma aka bar wuraren ibada da kasuwanni.
Bayan lura da gwamnatin tayi, ta bada shawarar a rufe wuraren ibada.Toh, nan fa wasu kuma suka taso da cewa dama ba wata cutar covid-19, kawai so ake a hana ibada, wai ai a wurin ibada ake amsar adduoi. Wannan dai mutane da yawa na ganin cewa jahiltan addini ne da tsabar son rai, ganin cewa Allah na amsar addu’o’i a ko ina.
A addinin musulunci dai, mun san ana hana wanda ya ci albasa ko tafarnuwa zuwa salla masallaci saboda warin zai cutar da masallta.Toh ina ga wanda ke dauke da cutar da ake dauka ta tari,shafa da sauran hanyoyin taruwa cikin jama’a,wanda kuma ba’a ga ne mai cutar sai takai wajen kwanaki 14? Har ila yau tsananin ruwan sama,sanyi ko tabo na hana zuwa masallaci a musulunci,wanda duk wanda yasan musulunci yasan haka kuma ya na kiyaye wa don gudun cutar da kansa.kawa dai son rai ya mantar da su ko kuma jahilci…
Cikin wani faifan audio,anji Sheikh Jingir na Jos na nuni da cewa ba wanda ya isa hana shi zuwa masallaci, tare da fadin cewa covid-19 farfagandan Turawa ne don hana Dawafi a makka (innanlillahi). Wannan tsagwaron rashin fahimtar abinda ke faruwa a duniya ne, wanda bai makamata ace yana fitowa daga bakin mallami irin sa ba. Ya kamata ya karfafa wa mabiya muhimmancin bin dokokin da malaman lafiya suka bada ta hannun gwamnati, Sannan ya dukufa wajen yin binciken da zai fahimta cutar da makasudin saka dokokin.
kamar yadda wasu jama’a ke ta korafin a rufe kasuwanne, gwamnatin jihar kaduna ta duba kuma ta dauki wasu tsauraran dokoki ciki harda rufe kasuwanni in banda shagunan saida magunguna da abinci.Saidai wasu talakawa da wasu masu kare hakkin al’umma sun juya suna korafin rufe shaguna,inda suke cewa yaya talaka zai samu abinci in ance an kulle shaguna!? Wannan batu gaskiya ne, kamar yadda akai fira da wasu shuwagabinin kungiyoyi masu zaman kan su a gidan radiyon DW.Sai dai abin lura anan shine: dole asa matakai don kare kai, kamar yadda gwamna El-Rufai ya bayyana lokacin bayanin matakan inda yace, babu ma’aikata da kayan aiki nayakin cutar covid-19, saboda haka mafita shine a kare kai kafin ta shigo. Ya kamata dai mu gane cewa, matakan sun zama dole ne ba wai don muzguna wa ba!
Wani abinda ke ta daure ma mutane kai ga me da covid-19 a Najeriya da kuma matakan da gwamntoci ke dauke shine na kusan ace halin ko in kula na wadanan rukunnan jama’a:
1 – Kamfanoni basa nuna jajircewar su wajen fadarkar da al’umma da ako yaushe ke rurubin siyan kayansu don amfanar juna. Duk da cewa wasu na kokarta wa, amma wasu sai da kawai ka ga suna tallar kamfanin su.Akwai yadda za su wayar wa mutane da kai bila adadin ta hanyar kafafen yada labarai musamman na rediyo don isar da sako nisa da kusa.Sanna zasu iya amfani da fostas da zane wurin fadarwa ga mutane masu raunin fahimta.
2 – Mafi yawancin ‘ya siyasar Najeriya sunyi gum da fararuwar wannan cutar, a lokacin da ya kamata su matso kusa da wadanda suka zabe su, su wayar musu da kai ta hanyar amfani da harshe da kafafen da mutanen su suka fi saurara ,ciki harda amfani da majigi da mai shela.Wannan lokaci da ake daukan matakai na kare kai da ya hada da rufe shagunan a jihar kaduna,shine daidai na raba kayan kare kai da kuma abin masarufi don tausaya wa. Amma ina, ko kadan ba muga alamar hakan ba! Sai dai muna fata.
3 – Kungiyoyi (NGOs) masu zaman kansu ma zuwa yanzu ba muga sun fara motsawa ba musamman abinda ya shafi tallafawa masu karamin karfa duba da matakan da gwamnatoci ke dauka. Duk da cewa ba kudi suke dashi ba,amma daga lalitar su baza arasa abinda za a taimaka ba,indai har al’ummar ake ma aiki.
4 – Su kuma talakawa da ake neman musu sauki a ko yaushe,abin takaici su ke kara kudin mota da na kayan masarufi don muzguna ma ‘yan uwan su talakawa. Da za ka hadu da su da kaji irin zagin da suke ma gwamnati da masu hannun da shuni cewa basu da tausayi.Abin tambaye shine:su tausayawar suke yi da suke tsawwala wa ‘yan uwansu talaka?
Sannan tsabar taurine kai na wasu talakawa wajen kin bin doka sai ya jefa su a halin ha’ula’i. kowa ya yadda da kaddara amma akwai sanadi .Idan malaman kiwon lafiya sun bada shawara,ya kamata kowa ya bi musamman talaka don shi ne ke shan wuya fiye da kowa.
Wannan na cikin iri koma bayar da muke samu a Najeriya,zagon kasa ta kowani fanni.
A kullum fatar mu gwamnati tayi kokarin taimaka wa talaka wurin samun abinda zai sa a bakin slati,musamman wannan lokaci na kafa dokoki don yakar covid-19.Su kuma masu hannu da shuni,su yi wa Allah su taimaka ma al’umma musamman makwafta. Talakawa suyi kokarin bin doka don zama lafiya.
Allah Ka yaye mana wannan cuta da sauran matsalolin Najeriya.
Khadijah Sulaiman.
Malama a tsangayar koyar da aikin Jarida a kwalejin kimiyya da fasaha dake zariya.
Khadijahsulaim93@gmail.co