Cutar COVID-19 cuta ce da tafi addabar sassan jikin dan adam dakeda alhakin musayan iska tsakanin cikin jikin mutum da wajen jikin mutum (wato atmosphere), musamman sassan jikin da da ake kira “hunhu”(lungs).
Kamar yanda aka sani a likitance, kwayoyin cuta(pathogenic microbes) suna daga cikin abubuwan dakan haddasa ciwuka a jikin Dan Adam.
To COVID-19 ma wata kwayar cuta ce mai suna SARS-CoV-2 ke haddasa ta. SARS-CoV-2 kwayar cuta ce kirar VIRUS. VIRUS sun kasance gida-gida ne, kuma kowace gida a karkashin ta akwai ‘ya’ya.
Toh SARS-CoV-2, ta fado ne a gida da ake kira “CoronaViruses Group”, wannan gida an sansu da haddasa ciwuka daban daban da yawanci ke addabar sassan jikin dan adam dake da alhakin musayan iska tskanin cikin jikin mutum da wajen jikin mutum(wato respiratory system).
Wasu daga cikin viruses din dake qasar wannan gida sun hada da Rhinovirus( wato qwayar cutar da ke kawo normal mura da muka sani), su SARS-CoV-1(da ya haddasa ballewar cutar SARS a shekarar 2002), da kuma su MERS-CoV(da ya haddasa ballewar cutar MERS a kasashen larabawa a shekarar 2012).
Wannan kwayar cuta an fara samun ta ne a garin Wuhan dake yankin Hubei na kasar China. An gano cewa a daa kwayar cutar jemage kadai take iya cutarwa, sai ta juya tana iya cutar da Pangolin, sai kuma tazo tana iya cutar da Dan Adam.
Cutar COVID-19 ya kasance cuta ne da ake iya yada ta tsakanin mutane, ma’ana, mai cutar zai iya yada wa marasa cutar suma su kama(infectious disease kenan). Idan mai cutar yayi tari ko atishawa, yakan saki wasu kananan halittu da ake kira “respiratory droplets” wanda kwayar cutar na manne dasu, wanda shine idan yashiga hancin mutum, ko bakinshi, ko idonshi ze iya kama wannan cuta.
Wainnan kananan halittu wato “respiratory droplets” sukan manne a iska, karafuna, hannu, roba da sauransu na wasu awanne kafin su lalace. Wannan kesa idan mutum ya shaka iskar dake dauke da wainnan halittu(respiratory droplets) ko ya taba daya daga cikin inda droplets dinnan suka manne da hannun shi kuma yakai hannun hanci, ko baki , ko ido zai iya kama wannan cutar!
Cutar bata cika nuna wasu alamu ba a cikin kwanaki biyar zuwa shida na farko (yakan kai sati biyu) na shigar kwayar cutar. Bayan wannan kwanaki, Alamomin cutar sun hada da zazzabi, tari, atishawa, numfashi sama sama, numfashi da kyar, gajiya/kasala, majina, makaki a wuya(sore throats), ciwon/zafin kirji da sauransu.
Mutum wanda kwayar cutar ta shiga jikinsa zai iya yada cutar cikin kwanakinnan na farko da alamomin cutar basu fara nunawa ba.
A yau mutane fiye da Dubu Dari Biyu ke kame da cutar bayan ta hallaka mutane fiye da Dubu Goma sha biyu a fadin duniya.
Hikimomin kare kai sun hada da;
1. Wanke hannu da ruwa da sabulu a kai kai, anfi so ruwan na zuba ne kaman daga famfo haka ko kuma wani nazuba ma mutum.
2. Yawaita amfani da sinadarin kashe kwayoyin cuta wato Hand Sanitizer musamman bayan gaisawa da sauran nau’ukan tabe tabe.
3. A guje wa yawaitan taba fuska, baki, hanci da ito da hannu.
4. Idan mutum zai yi atishawa ko tari, kada ya tare da tafin hannunsa, ya lanqwasa hannunsa yayi tarin ko atishawar a wajan gwuiwar hannu.
5. Yanada matukar mahimmaci a rage taron mutane daya a waje daya musamman a inda aka tabbatar da wannan cuta.
6. Killace kai yanada matukar mahimmanci saboda mun yi bayani yanda mutum daya mai cutar zai iya yada cutar tun kafin shi kanshi yasan yana da cutan! Kuma kwayoyin cutar sukan manne a iska, karfe, roba da sauransu na tsawon wasu awanni kafin su mutu. Saboda wannan yanayi nacewa mutum mai cutar bai sanin yanada cutar a farko kuma yana yada ta, hikima ce mai kyau mutune su killace kansu musamman a kasashen da aka tabbatar da wannan cuta. A saboda da rashin killace kai ne wata yar kasar China ta zama silar kamuwar mutane fiye da 5000 da wannan cuta a kasar Koriya ta Kudu, South Korea.
7. Yanada matukar mahimmanci a tuntumbi hukumar NCDC a duk lokacinda aka lura da wani na dauke da alamomin wannan cuta ko aka tabbatar yayi tafiya zuwa daya daga cikin kasashen da cutar tayi tasiri sosai kuma yadawo be killace kanshi ba.
Wa tawakkal Alallah!
Daga Abdulhaleem Ishaq Ringim,RN(ABUTH)
Haleemabdul1999@gmail.com
08036189935(WhatsApp kadai)