Ministan kiwon lafiya Osagie Ehanire yace gwamnati baza ta kafa dokar hana shige da fice daga waje ko daga cikin kasar nan ba.
Ehanire ya fadi haka da yake zantawa da manema labarai ranar Juma’a a Abuja.
Ya ce cutar bata yadu a kasar nan ba da har zai tada wa mutanen kasar hankali da gwamnati shi ne yasa za a ci gaba da kyale jirage na sauka, suna tashi a Najeriya, duk da kuwa cutar ta yi kamari a wasu kasashen duniya.
Ehanire yace duk da haka gwamnati za ta ci gaba da karfafa matakan hana yaduwar cutar a tashoshin jiragen sama sannan ta hada hannu da hukumar hana shige da fici da hukumar kwastam domin ganin an hana cutar shigowa kasar nan.
Bayan haka bada bayanan halin da wadanda suka kamu da cutar a kasar suke ciki.
Ya ce mutum na biyu da ya kanu da cutar ta hanyar baItaliyan da ya shigo Najeriya da cutar ya gama samun sauki. Yan zu ana duba shi a tabbayar ya warke kafin a sallameshi.
Sannan shima dan kasar Italiya da ya shigo da cutar na samun sauki sannan nan ba da dadewa ba za a sallame shi daga asibiti.
Idan ba a manta ba a wannan mako ne kungiyar kiwon lafiya ta duniya (WHO) ta sanar cewa coronavirus ta zama annoba a duniya.
Cutar ta yadu zuwa kasashe 118 sannan mutane 125,000 sun kamu da cutar a duniya.
A dalilin haka kasashen duniya kamar su Amurka,Saudiya,Italiya da sauran su suka rufe iyakokin su ga duk wani bako.