CORONAVIRUS: Za a rufe makarantun Arewa maso Yammacin Najeriya na kwana 30

0

A wani zama da kungiyar gwamnonin yankin Arewa maso yammacin kasar nan suka yi ranar Laraba a garin Kaduna sun bayyana cewa gwamnonin sun yanke hukuncin a rufe makarantu na yankin zuwa kwanaki 30 masu zuwa.

Shugaban kungiyar kuma gwamnan jihar Katsina Aminu Masari ya sanar da haka wa manema labarai bayan an tashi taron.

Masari ya ce daukan matakan dakile yaduwar coronavirus a yankin ya zama dole duk da cewa cutar ba ta bullo a yankin ba sannan sakamakon gwajin cutar da aka yi wa wasu mutane a yankin da ake zargin sun kamu da cutar ya nuna basu dauke da ita.

Ya ce za a rufe makarantun daga ranar Litini 23 ga watan Maris 2020 na tsawon kwanaki 30.

Masari ya kuma ce za a ci gaba da wayar wa mutane kai mutane game da cutar da kuma yadda za su kiyaye ta hanyar tsaftace muhalli da kawunan su.

Kungiyar ta kuma tattauna bude asusu domin tara kudaden kawar da rashin tsaron da ya mamaye yankin.

Gwamnan jihar Kebbi Atiku Bagudu, gwamnan jihar Jigawa Abubakar Badaru, gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai, gwamnan jihar Sokoto Aminu Tambuwal, gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle da gwamnan jihar Niger Abubakar Sani Bello na cikin gwamnonin da suka halarci zaman.

Ma’aikatan kiwon lafiya ta sanar cewa mutane takwas ne suka kamu da coronavirus a kasar nan.

Daga cikin wadannan mutane akwai jaririya ‘yar wata shida da ta kamu da cutar.

An kuma gano wani dake dauke da cutar da ya shigo ta iyakan iyakar Najeriya da wasu kasashe ta kasa.

Sannan duk sauran wadanda suka kamu suna da tarihin zuwa kasashen Amurka da Uk.

A yau Laraba ne ma’aikatar kiwon lafiya ta sanar cewa wasu mutane biyar sun kamu da cutar coronavirus a kasar nan.

Bincike ya nuna cewa mutane biyar din da suka kamu da cutar sun yi tafiya zuwa kasashe Amurka da UK.

Sannan ranar Talata ne ma’aikatar kiwon lafiya ta jihar Legas ta sanar cewa wata ‘Yar Najeriya ta kamu da cutar coronavirus.

Wannan yarinya ta dawo daga kasar Birtaniya ne idan bayan bata ji dadin jikinta ba ta killace kanta sannan daga baya ta je asibiti domin a duba ta. Nan ne aka gano ta kamu da cutar coronavirus.

Duk da cewa an yanzu mutane uku ne aka tabbatar sun kamu da cutar sai dai daya daga cikin su gwaji ya nuna cewa Bashir dauke da wannan cuta.

Wani Dan kasar Italiya ne ya shigo Najeriya da cutar, inda daga baya aka samu wani Shima sake da alamun wannan cuta to sai kuma mutum na uku da aka gano yanzu data shigo kasa daga Birtaniya.

Kwayoyin cutar Corona Virus na daga cikin kwayoyin cutar dake sa a kamu da mura wanda idan yayi tsanani akan yi fama da matsalar cutar dake hana numfashi yadda ya kamata da ake kira (Middle East Respiratory Syndrome (MERS-CoV), da kuma cutar tsanannin mura da kan toshe makogoro.

Alamun kamuwa da cutar sun hada da matsala a kafofin wucewar iska a makogoro wato numfashi, yawan zazzabi, tsananin tari, da ciwo a makogoro.

Idan abin yayi tsanani, ya kan kai ga shakar iska ma ya gagara, sannan a samu matsalar sanyin hakarkari wato ‘Nimoniya’, kuma idan har ya yi tsanani matuka kodar mutum kan daina aiki kwata-kwata.

Za a iya kaucewa kamuwa da wannan cuta ta hanyar, yawaita wanke hannaye da ruwa da sabulu, sannan a rika rufe hanci da baki idan za ayi atishawa kuma a rika wankewa da dafa nama sosai ya nuna tubus kafin a ci da kwai.

A rika nisanta ko kuma zama kusa da wanda ya nuna alamun rashin lafiya musamman irin wadanda a ka lissafa a sama sannan a gaggauta zuwa asibiti da neman magani idan ba a da lafiya.

Cutar da ta samo asali a kasar Chana a watan Disemba 2019 ya kama mutane 80,849 sannan da dama sun mutu a kasar.

Coronavirus ta yaduwa zuwa wasu kasashen duniya inda mutane 157,208 sun kamu da cutar wasu 5,842 sun mutu a kasashen duniya 153.

A yanzu dai kasashen Italiya da Masar a Najiyar Afrika na cikin kasashen da wannan cutar ta yi wa kamun farad daya.

Share.

game da Author