Ministan babban birnin tarayya Abuja Muhammed Bello ya bayyana cewa gwamnati za ta kara yawan wuraren kula da wadanda suka kamu da cutar coronavirus a Abuja.
Bello yace idan har ya kama gwamnati za ta maida babban asibitin dake Zuba asibitin kula da wadanda suka kamu da cutar.
Kakakin ministan Anthony Ogunleye ya sanar da haka a wata takarda da aka raba wa manema labarai a daren Talata.
Bisa ga takardar, minista Bello ya ce gwamnatin ta hada hannu da asibitin koyarwa dake Gwagwalada domin fadada cibiyar kula da mutanen da suka kamu da coronavirus yadda zai dauki mutane da yawa.
Bayan haka a ranar Litini shugaban kungiyar malaman jami’o’I na kasa (ASUU) Biodun Ogunyemi yace za a maida sashen kula da mutane masu neman kula na gaggawa asibitin koyarwa na jami’ar Abuja wajen kula da mutanen da suka kamu da coronavirus.
Karamar Ministan Abuja Ramatu Aliyu ta ce gwamnati za ta ziyarci mutane a kananan hukumomi domin wayar da kan mutane game da cutar da hanyoyin samun kariya daga cutar.
Abuja ta rufe kasuwaninta ne bayan gwamnan jihar Legas Babajide Sanwo-Olu ya rufe kasuwanin jihar ranar Talata domin hana yaduwar cutar a jihar.
A Abuja mutane takwas suka kamu da cutar inda a ciki akwai shugaban Ma’aikatan fadar shugaban kasa Abba Kyari wanda aka killace bayan an tabbatar da ya kamu da cutar.
Hanyoyi 10 da za a kiyaye domin kare kai daga CORONAVIRUS.
1 – A rika Wanke hannuwa da sabulu a duk lokacin da aka dan wataya ko kuma aka yi tabe-taben abubuwa. Ko bako Kayi ka bashi dama ya wanke hannu kafin ku fara mu’amala.
2 – Ku rufe hanci da bakinku lokacin da kuke yin atishawa da gefen Hannu amma ba da tafin hannu ba. Idan kun shafi bakunan ku toh, ku wanke hannu maza-maza.
3 – A daina taba idanuwa da hannaye ko kuma hanci da baki. Ka du rika yawan shafa fuskokinku da hannaye. Idana an yi haka a gaggauta wanke hannaye.
4 – A nisanci duk wani da bashi da lafiya, musamman mai yin Mura da tari. Ko zazzabi ne yake yi a nisanta da shi sannan a bashi magani da wuri. Idan abin ya faskara a gaggauta kaishi asibiti domin a duba shi.
5 – A kula da yara sannan a rika tsaftace muhalli.
6 – A rika gaisawa da juna nesa-nesa
7 – Idan kayi bako daga kasar waje, kada a kusance shi koda dan uwana ne sai ya killace kan sa na tsawon makonni biyu.
8 – A rika Karantar da yara yadda za su kiyaye koda an aike su a waje.
9 – A yawaita cin abinci masu gina jiki, shan ruwa da motsa jiki.
10 – A yawaita yin addu’a da sadaka.
Discussion about this post