CORONAVIRUS: Yadda Gwamnoni suka karbe ayyukan Shugaban Kasa, Kowa ta sa ta fisshe shi

0

A irin wannan mawuyacin halin da ake bukatar Buhari a matsayin sa limamin gwamnoni ya shiga gaba domin gyaran rafkanuwa, sai ya lamfale a Fadar Shugaban Kasa, su kuma gwamnoni kowa ya mike tsaye ya na gaganiyar yin ta sa rafkanuwar, wadda liman ne ya cancanci ya gyara musu bai-daya.

Kowa Ta Sa Ta Fisshe Shi

A Kano, Gwamna Umar Ganduje ya rufe kan iyakokin jihar ruf tare da rufe filin saukar jirage. Shi ma gwamnan Delta, Ribas da Nasir El-Rufai na Kaduna duk sun rufe na su jihohin, domin hana cutar Coronavirus barkewa a jihohin.

Yayin da ake ta karankadakaliya da fafutikar yadda za a hana Coronavirus barkewa a Najeriya, Buhari ya yi kwanciyar sa, kai ka ce barci da minshari ya ke yi, domin sai a shafe lokuta ko duriyar sa ba a ji ba.

Su kuma gaamnoni, kowa ya dauki matakin kafa dokokin kowa-tasa-ta-fisshe-shi. Wannan kuwa karara na nuni da cewa akwai gagarimar matsakar shugabanci a bangaren Buhari.

A ranar 28 Ga Maris, an samu adadin wadanda su ka kamu da cutar a Najeriya har mutum 89, amma har yau Shugaba Muhammadu Buhari bai yi tunanin kafa dokar-ta-baci ba. Sai dai gwamnoni ke ta hakilon yadda za su kubutar da al’ummar jihohin su.

Duk da kiraye-kirayen da ake yi wa Buhari ya sa dokar-ta-baci, bai yi haka nan din ba. Dama wannan halin sa ne, sau da yawa ba ya daukar wani kwakwaran mataki sai ya ga jama’a sun fito a kafafen yada labarai su na ragargazar sa.

Dokar Najeriya ta 36 da ta 63, ta mika ikon kan iyakokin kasar nan na sama, na ruwa da na kasa kacokan a kan shugaban kasa, ba kan gwamnoni ba.

Idan Ba Ka Yi Ba Ni Wuri

Gwamnan jihar Rivers ne ya fara tashi ya kafa dokar hana shiga jihar ta ruwa, ta kasa ko ta sama gaba daya a ranar 26 Ga Maris.

KANO: Duk da cewa har yau ba a samu wanda ya kamu a Kano, jihar da ta fi saura yawan jama’a banda Lagos ba, duk da haka sai Gwamna Ganduje ya hana shiga jihar daga sauran jihohi. Kafin sannan kuma sai da ya hana manyan motoci masu saukar dandazon fasinjoji shiga Kano.

Mako daya kafin sannan kuma dama gwamnatin sa ta bada umarnin kowane malamin makarantat alla ya maida almajirin da ke karkashin a wurin iyayen sa, can a garin da almajirin ya fito.

DELTA: Shi ma Gwamna Okowa tun a ranar 26 Ga Maris ya hana shiga jihar. Washegari kuma ranar 27 Ga Maris, ya rufe filin jirgin zaman Asaba, babban birnin jihar, ya ce daga ranar 29 Ga Maris, babu jirgin da za a bari ya sake sauka Asaba.

Jihohin Ebonyi, Akwa Ibom, Jigawa, Sokoto da Anambra kowace ta shigo da irin dokokin ta daban-daban.

Najeriya ta yi fama da barkewar annoba a baya-bayan nan, irin su Zazzabin Lassa da sauran su. To amma bullowar cutar Coronavirus ne ya fi firgita kasar, musamman saboda ganin irin mummunar barnar da cutar ke yi, ko ta ke yi a China, Turai da Amurka.

Abdul Mahmud ya bayyana cewa Dokar Killace Jama’a A Lokacin Annoba ta 1926, ta bai wa gwamnoni ikon daukar matakan gaggawa, a inda shugaban ba ya nan, ko kuma ya na nan, amma ya hi jan-kafa wajen gaggauta daukar kwakkwaran matakan da su ka wajaba ya dauka.

KADUNA: Gwamna El-Rufai ne ya fara daukar irin wannan kwakkwaran mataki na irin na Dokar 1926, inda ya tilasta kowa ya killace kan sa a gida. Sannan kuma ya haramta shiga masallatai da coci a yi bauta a cikin su.

El-Rufai ya kara da yin kurarim cewa duk masallacin da aka bude aka yo sallar Juma’a, ko cocin da aka yi bauta a ciki, to za a rushe su.

Buhari: Likimo Ko Boyo Ya Yi?

Rabon da Buhari ya fito halartar wani taro tun a ranar 19 Ga Maris, inda ya halarci taron bude wasu layukan tarho na tarayya a Abuja. Can din ma bai jima ba.

Wannan ya sa jama’a da dama ke cike da waswasin shin Shugaba Buhari lafiya ya ke kuwa?

Duk da wannan tunani da ‘yan Najeriya ke yi, Buhari ya yi zaman sa, sai dai kakakin yada labaran sa biyu, su ne ke fitar da bayanai da sunan Shugaba Buhari ya ce, ya bayyana, ya yi kira, ya roki, ya yaba, ko kuma ya nuna rashin jin dadin kaza da kaza.

Share.

game da Author