An bayyana mutuwar Lorenzo Sanchez, tsohon shugaban kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid da ke Spain.
Ya rasu a asibiti bayan an garzaya da shi, sakamakon kamuwa da cutar Coronavirus a ranar Asabar da ta gabata.
Kafofin yada labarai na Spain, irin su Marca da kuma BBC, CNN da sauran jaridun Turai suka tabbatar da rasuwar Sanchez, ta bakin dan sa, Farnado.
Sanchez mai shekara 76 kafin mutuwar sa, ya yi shugabannin Real Madird tsawon shekaru biyar, daga 1995 zuwa 2000.
Bayan ya sauka ne aka zabi Florentina Perez, wanda ke kai har yau din nan.
A zamanin Sanchez, Madrid ta ci kofin Champions League har sau biyu.
Kuma dan sa Fernando shi ma ya buga wa Madrid kwallo tsakanin 1996 zuwa karshen kakar 1999, inda ya koma Real Malaga.
Da ya ke sanar da mutuwar mahaifin na sa, ya bayyana cewa ya yi bakin cikin yadda cutar ta kashe mahaifin sa Sanchez, ganin yadda ya bayar da gudummawa a rayuwar sa, amma aka kasa ceto rayuwar sa.
Sanchez ya ajiye tarihi a Real Madrid, wanda baya ga ciwo kofin Champions League biyu da ya yi, shi ne kuma ya sayo wasu mashahuran ‘yan wasa irin su Roberto Carlos, Clearance Seedof, Favor Sukar da sauran su.
Tuni dai Real Madrid ta bayyana jimami da alhini da takaicin rashin Lorenzo Sanchez sanadiyyar Coronavirus.
Cutar Coronavirus ta yi muni a kasar Spain, domin a can ta fi muni a Turai, in banda kasar Italy.
PREMIUM TIMES HAUSA ta bada labarin wasu fitattun ‘yan wasa da suka kamu da cutar Coronavirus, ciki har da Paolo Dybala na Juventus, tsohon dan wasan AC Milan, Paulo Maldini da Fellani, tsohon dan wasan Manchester United.
Discussion about this post