Rundunar Sojojin Najeriya ta bayyana wasu tsauraran matakan da za ta dauka domin hana cutar Coronavirus ci gaba da fantsama a kasar nan.
Cikin wata samarwar da Babban Daraktan Tsare-tsare, Laftanar Janar Lamidi Adeosun ya sa wa hannu, za a fara tirsasa wa jama’a yin zaman dirshan a gida har zuwa lokacin da gwamnati ta bayyana a ci gaba da harkoki kamar kullum.
Sannan kuma sojoji za su rika tirsasa kai mai cutar Coronavirus zuwa asibiti ko da arziki ko da tsiya.
Wannan shiri mai suna ‘Operation Second Eleven’, ya hana sojoji su kan su yawan taruwa cunkus a wuri daya, sannan kuma an soke duk wasu taruka da aka tsara gudanarwa cikin 2020, kafin a ga yadda hali ya yi.
Sojoji za su rika gadin manyan kantinan sayar da kayan abinci da suto-suto na ajiyar abincin gwamnati, gudun kada batagari ko barayi su fasa kantinan ko rumbunan ajiyar abincin.
Sojoji sun soke batun masu tafiya duk wata kasa domin halartar taruka na spja ko wasu kwasa-kwasan soja.
Sannan kuma an rufe duk wasu makarantun sojoji da cibiyoyi. Kuma an dakatar da taron gabatar da sojojin Rukunin 420 na Kwalejin Yankin Soja da aka shirya yi.
Sojoji sun rage lokacin aikin jami’an su, sannan kuma an takaita kai ziyara cikin sojoji da yawan karakaina musamman a hedikwatar soja.
Sanarwar ya kuma gindaya wa sojoji ka’idoji da matakan kare kai daga kamuwa daga cutar Coronavirus.