CORONAVIRUS: Saudiyya ta dakatar da sallolin jam’i da Juma’a a masallatan Kasar

0

Mahukuntan kasar Saudiyya sun sanar da dakatar da yin sallolin jam’i da sallar Juma’a a duka masallatan kasar domin dakile yaduwar cutar coronavirus da yake yaduwa kamar wutar daji a kasashen duniya.

Gwamnati ta bayyana cewa wannan doka bai shafi masallatan Makka da Madina ba.

Kwamitin gudanarwar Kasar Saudiyya ta ce za a rika kiran sallah kamar yadda ake yi a kullum amma ba za a je masallaci ba, kowa zai rika Sallah a gidan sa ne.

An samu wadanda suka kamu da cutar 38 cikin kwana daya a kasar da hakan ya sa yawan wadanda suka kamu ya kai 171 a kasar.

Bayan haka gwamnati ta dakatar da taruwa da ake yi ana koyon karatu da karatun Qur’ani a kasar saboda wannan annoba.

Sannan kuma kamfanoni masu zaman kansu a Kasar sun umarci ma’aikatan su dasu yi aiki daga gida daga yanzu.

Coronavirus

Kwayoyin cutar Corona Virus na daga cikin kwayoyin cutar dake sa a kamu da mura wanda idan yayi tsanani akan yi fama da matsalar cutar dake hana numfashi yadda ya kamata da ake kira (Middle East Respiratory Syndrome (MERS-CoV), da kuma cutar tsanannin mura da kan toshe makogoro.

Alamun kamuwa da cutar sun hada da matsala a kafofin wucewar iska a makogoro wato numfashi, yawan zazzabi, tsananin tari, da ciwo a makogoro.

Idan abin yayi tsanani, ya kan kai ga shakar iska ma ya gagara, sannan a samu matsalar sanyin hakarkari wato ‘Nimoniya’, kuma idan har ya yi tsanani matuka kodar mutum kan daina aiki kwata-kwata.

Za a iya kaucewa kamuwa da wannan cuta ta hanyar, yawaita wanke hannaye da ruwa da sabulu, sannan a rika rufe hanci da baki idan za ayi atishawa kuma a rika wankewa da dafa nama sosai ya nuna tubus kafin a ci da kwai.

A rika nisanta ko kuma zama kusa da wanda ya nuna alamun rashin lafiya musamman irin wadanda a ka lissafa a sama sannan a gaggauta zuwa asibiti da neman magani idan ba a da lafiya.

Cutar da ta samo asali a kasar Chana a watan Disemba 2019 ya kama mutane 80,849 sannan da dama sun mutu a kasar.

Coronavirus ta yaduwa zuwa wasu kasashen duniya inda mutane 157,208 sun kamu da cutar wasu 5,842 sun mutu a kasashen duniya 153.

A yanzu dai kasashen Italiya da Masar a Najiyar Afrika na cikin kasashen da wannan cutar ta yi wa kamun farad daya.

Share.

game da Author