CORONAVIRUS: Sama da mutane 500,000 ne suka kamu a Duniya

0

Sakamakon rahoton ‘Worldometer’ dake yin kididdigar yaduwar cutar coronavirus ya nuna cewa mutane 566,064 sun kamu da cutar a fadin duniya zuwa yanzu.

Rahoton ya nuna cewa akalla mutane sama da 25,000 sun mutu a dalilin wannan cuta sannan mutane sama da 300,000 sun warke daga cutar a duniya.

A kasar Amurka, Akwai akalla mutane sama da 93,151 da suka kamu da cutar sai Kasar Chana da mutane 80,340 sai kasar Italiya.

Kasar Italiya ta rasa mutane sama da 8, 215, mutane 3, 292 sun mutu a kasar Chana sannan Amurka ta rasa mutane 1,382.

Worldometer ta rawaito cewa ranar Juma’a a cikin minti 20 mutane 10,000 sun kamu da cutar a duniya.

Babu wanda ke da masaniyar adadin yawan mutanen dake dauke da cutar a duniya domin kasashe da dama sun koka da karancin kayan gwajin cutar.

NAHIYAR AFRIKA

Kasashen Afrika 46 daga cikin 54 ne ke fama da cutar a Nahiyar Afrika.

A Najeriya mutane 70 ne ke dauke da cutar, mutum uku sun warke sanan daya mutu.

An gano haka ne a jikin wasu mutane 14 da suka kamu da cutar inda 12 na jihar Legas sannan 2 a Abuja.

Masana kimiya sun yi kira ga kasashen Afrika da su gaggauta daukan tsauraran matakan hana yaduwar cutar ganin cewa babu ingantattun fannin kiwon lafiya, sannan zai yi wahala matuka wajen hana mutane walwala da tarurruka.

Share.

game da Author