CORONAVIRUS: Sakamakon gwajin Muhammadu Sanusi da ya fito

0

Daya daga ciki ‘ya’yan tsohon sarkin Kano, Muhammadu Sanusi, Ashraf Sanusi ya bayyana cewa mahaifin sa tsohon Sarki, Sanusi ba ya dauke da cutar coronavirus.

Ashraf ya bayyana haka a shafin sa ta tiwita, in da ya ce tun a ranar 25 ga
watan Maris aka dauki samfarin gwajin
iyayen sa domin yin gwaji kuma ko da
sakamako ya fito, babu alamun wannan
cuta a tattare da su.

Ashraf ya bayyana a shafin sa ranar 25 ga wata wanda BBC Hausa ta wallafa a shafinta cewa kaf iyalan tsohon Sarki basu dauke da wannan cuta.

Tun bayan da gwamnan Kaduna Nasir E-Rufai ya bayyana cewa ya kamu
da cutar coronavirus, jama’a da dama
suka rika cewa akwai yiwuwar kila tsohon Sarkin Kano Muhammadu Sanusi
II na dauke da cutar shima saboda yadda suka rika cudanya da juna a lokacin da aka tsige shi daga sarautar Kano da kuma kusancin su.

Sakamakon gwajin ya nuna baya dauke da cutar tare da sauran iyalan da.

A Najeriya, gwamnoni biyu aka tabbatar sun kamu da cutar, Nasir El-Rufai, na jam’iyyar APC, da Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohamed na jam’iyyar PDP.

Gaba dayan su na killace ana duba su.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari zai Yi wa yan kasa jawabi a ranar Lahadi da karfe 7 na yamma.

Share.

game da Author