Hukumar kula da dalibai masu yi wa kasa hidima (NYSC) ta dakatar da horas da dalibai masu yi wa kasa hidima na Rukunin A na shekarar 2020 a duk sansanonin Najeriya.
Hukumar ta kuma rarraba wa daliban wasikun tura su wuraren da za su yi aikin yi wa kasa hidimma.
NYSC ta yi haka ne domin hana yaduwar cutar coronavirus da ta bullo a kasar.
Wani dake yi wa kasa hidima a jihar Gombe ya ce tun da karfe 1 na dare jami’an hukumar suka sanar cewa an rufe sansanin, kowa ya zo ya karbi wasikar tura shi inda zai yi aikin bautan.
Wata kuwa dake bautan kasa a jihar Filato ta ce da sanyin safiyar Laraba suka samu sanarwan dakatar da horas da daliban.
Bayanai sun nuna cewa wannan mataki da hukumar ta dauka na da alaka da hukuncin hana jami’an gwamnatin fita zuwa kasashen waje da kwamitin shugaban kasa kan dakile yaduwar cutar ta sanar ranar Talata.
Kwamitin ta kuma gargaddi mutane da su rage yawan shiga taruka domin kada a samu yaduwar cutar.
Sai dai kuma wannan doka da aka kafa bai hana baki daga kasashen da wannan cuta ta yi wa katutu ba shigowa kasar sai dai kawai idan suka shigo dole su killace kansu har sai sun yi kwanaki 14 tukunna.
A yau Laraba ne ma’aikatar kiwon lafiya ta sanar cewa wasu mutane biyar sun kamu da cutar coronavirus a kasar nan.
Bincike ya nuna cewa mutane biyar din da suka kamu da cutar sun yi tafiya zuwa kasashe Amurka da UK.
Sannan ranar Talata ne ma’aikatar kiwon lafiya ta jihar Legas ta sanar cewa wata ‘Yar Najeriya ta kamu da cutar coronavirus.
Wannan yarinya ta dawo daga kasar Birtaniya ne idan bayan bata ji dadin jikinta ba ta killace kanta sannan daga baya ta je asibiti domin a duba ta. Nan ne aka gano ta kamu da cutar coronavirus.
Duk da cewa an yanzu mutane uku ne aka tabbatar sun kamu da cutar sai dai daya daga cikin su gwaji ya nuna cewa Bashir dauke da wannan cuta.
Wani Dan kasar Italiya ne ya shigo Najeriya da cutar, inda daga baya aka samu wani Shima sake da alamun wannan cuta to sai kuma mutum na uku da aka gano yanzu data shigo kasa daga Birtaniya.
Kwayoyin cutar Corona Virus na daga cikin kwayoyin cutar dake sa a kamu da mura wanda idan yayi tsanani akan yi fama da matsalar cutar dake hana numfashi yadda ya kamata da ake kira (Middle East Respiratory Syndrome (MERS-CoV), da kuma cutar tsanannin mura da kan toshe makogoro.
Alamun kamuwa da cutar sun hada da matsala a kafofin wucewar iska a makogoro wato numfashi, yawan zazzabi, tsananin tari, da ciwo a makogoro.
Idan abin yayi tsanani, ya kan kai ga shakar iska ma ya gagara, sannan a samu matsalar sanyin hakarkari wato ‘Nimoniya’, kuma idan har ya yi tsanani matuka kodar mutum kan daina aiki kwata-kwata.
Za a iya kaucewa kamuwa da wannan cuta ta hanyar, yawaita wanke hannaye da ruwa da sabulu, sannan a rika rufe hanci da baki idan za ayi atishawa kuma a rika wankewa da dafa nama sosai ya nuna tubus kafin a ci da kwai.
A rika nisanta ko kuma zama kusa da wanda ya nuna alamun rashin lafiya musamman irin wadanda a ka lissafa a sama sannan a gaggauta zuwa asibiti da neman magani idan ba a da lafiya.
Cutar da ta samo asali a kasar Chana a watan Disemba 2019 ya kama mutane 80,849 sannan da dama sun mutu a kasar.
Coronavirus ta yaduwa zuwa wasu kasashen duniya inda mutane 157,208 sun kamu da cutar wasu 5,842 sun mutu a kasashen duniya 153.
A yanzu dai kasashen Italiya da Masar a Najiyar Afrika na cikin kasashen da wannan cutar ta yi wa kamun farad daya.
Discussion about this post