CORONAVIRUS: Najeriya ta shiga uku sau uku, farashin gangar danyen mai ya koma dala 18 kacal

0

Yayin da kasashen duniya manya da kanana ke ta gaganiyar kakkabe cutar Coronavirus, farashin gangar danyen man fetur ya sake faduwa kasa warwas a duniya, har zuwa dala 18.

Wannan mummunar faduwa da farashin danyen mai ya yi a duniya ya tada hankalin komai a duniya, musamman ma Najeriya wadda ta dogara kacokan da danyen mai wajen gudanarwa da tafiyarwar harkokin gwamnati.

Yayin da danyen mai ta fado zuwa dala 20 tun cikin 2002, zamanin mulkin Olusegun Obasanjo.

Babban dalilin faduwar darajar farashin danyen mai a duniya shi ne fantsamar cutar Coronavirus wadda ta tsaida zirga-zirgar jiragen sama, na ruwa da motoci da kuma tsaida ayyuka a masana”anru manya da kanana a fadin duniya.

A ranar Litinin an saida danyen mai samfurin Brent a kan dala 22.58. Rabon da farashin ya yi warwas tun cikin 2002.

Farashin irin na Amurka ya fi faduwa zuwa dala 20 kacal. Tun a farkon barkewar Coronavirus ce farashin gangar danyen mai ke ta yin kasa, bai sake yin sama ba

Najeriya Ta Shiga Uku Sau Uku

Tun ma lokacin da farashin ya fara yin kasa ne Najeriya ta yi sanarwar cewa ba taiya aiwatar da kasafin kudi na 2020 gaba daya ba.

Kasafin wanda aka tsara shi a kan farashin litar gangar mai dala 57, an zabtare shi da kashi 50% bisa 100% a kan dala 30.

To yanzu kuma farashin danyen mai ya sake yin kasa, zuwa kasa da dala 20 a kasuwar duniya.

Najeriya ta tsara kashe naira tiriliyan 10.59 cikin 2020. Daga cikin kudin, naira tiriliyan 2.72 duk wajen biyan bashi duk za a kashe su. Sannan kuma naira tiriliyan 2.46 ne kadai za a yi wa jama’a aiki da su.

Idan za a tuna, Najeriya ta ce marukar farashin danyen mai ya fadi zuwa ko da dala 22 ce, to za ta daina hako danyen mai domin ko ta hako asara za ta yi, babu riba.

Najeriya na kashe dala 15 zuwa 17. Don haka ko an hako danyen man faduwa za a yi warwas, ba riba za a ci ba.

PREMIUM TIMES ta bada rahoton yadda Coronavirus ta kamo hanyar durkusar da tattalin arziki Najeriya

Wata tattaunawa da aka yi ta kai-tsaye da wasu masana tattalin arziki su biyu, sun bayyana cewa, tattalin arzikin Najeriya ba wai matsala ce kadai zai fuskanta ba idan aka ci gaba da fuskantar annobar Coronavirus. Sun ce rugujewa ce ma tattalin arzikin zai yi.

Sun ce ba daidai ba ne da Ministar Harkokin Kudade, Zainab Ahmed ta ce za a fuskanci matsin tattalin arziki. Inji su, kamata ya yi ta fito karara ta ce za a fuskanci rugujewar tattalin arziki.

Masani Tope Fasua, Shugaban Global Analytics Consulting Limited da ke Abuja, shi da Paul Aladje na SM Professionals, sun ce ai idan ana batun matsin tattalin arziki ne, tuni Najeriya ta rigaya ta afka cikin matsin tattalin arziki, domin an daina sarrafa kayayyaki, ma’aikatan ofis da majiya karfi masu aiki a masana’antu duk sun koma gida sun zauna.

“Bankin Bada Lamuni na Duniya IMF ya ce a duniya an daina sarrafawa da kara kashi 80 bisa 100 na kayan da ake samarwa saboda Coronavirus. To me ya rage kuma?

Ba Za Mu Iya Jure Watanni Shida A Killace Ba -Ministar Harkokin Kudade

Ministar Harkokin Kudade Zainab Ahmed ta ce Najeriya za ta iya jure tsawon watanni uku a cikin mawuyacin halin da aka shiga saboda Coronavirus.

Amma kuma ta ce a gaskiya idan aka kai tsawon watanni ahida, to kasar za ta afka cikin halin matsin tattalin arziki ne kawai.

Tuni dai farashin danyen man fetur ya karye warwas, har ta kai ga Shugaban Hukumar NNPC na cewa idan farashin danyen mai ya gaba da karyewa a duniya, to Najeriya za ta daina hako danyen mai, domin ko an hako, to faduwa za a yi, maimakon a ci riba.

Masana Fasua da Aladje sun bayyana cewa Karfin Tattalin Arzikin Najeriya (GDP) bai wuce dala bilyan 450 ba. Sannan kuma a yanzu a kullum kasar na asarar dala bilyan milyan 400 a kowace rana.

Saboda haka inji su, a wata za a yi asarar dala bilyan 12 kenan, saboda harkokin kasuwanci na cikin gida da waje duk sun tsaya cak.

“Akalla majiya karfi milyan 80 ke gida zazzaune babu aiki, saboda Coronavirus ta tsaida komai.

“Don haka idan aka tafi a haka, durkushewa ce ma tattalin arziki kasar nan zai yi, ba wai matsin tattalin arziki ne kadai za a fuskanta ba, kamar yadda iya Ministar Harkokin Kudade ta bayyana.” Inji su biyun.

Najeriya Ta Kusa Daina Hako Fetur Saboda Coronavirus -Shugaban NNPC

Faduwar farashin danyen man fetur a duniya na daf da tilasta wa Najeriya dakatar da hako danyen mai har sai yadda hali ya yi.

A ranar Litinin da ta gabata, an dibga asarar farashin gangar danyen mai, ta yadda farashi a Kasuwar Hada-hadar Turai ta ICE Futures Europe Exchangr, ya kara faduwa warwas daga dala 25.82 kowace gangar danyen mai, ya sake raguwa da dala 1.16, wato zuwa dala 24.68 kenan na kowace gangar danyen man fetur a ranar Juma’ar da ta gabata.

‘Mun Bani Mun Lalace’ -Shugaban NNPC
Shugaban Hukumar Kula Da Harkokin Fetur (NNPC), Kyari, ya nuna matukar firgita dangane da faduwar farashin danyen man fetur.

Ya nuna cewa matsawar farashin ya sake yin kasa, ya ragu da ko da dala 3 ce daga yadda ya ke a yanzu, to Najeriya ba ta da wani zabi sai dai kawai ta daina hako mai, har sai yadda Allah ya yi.

“Idan har farashin gangar danyen mai ya kara yin kasa, ya koma dala 22 kowace ganga, to kasashen irin su Najeriya sai dai su zauna, su daina hako mai, domin ko an hako din ma asara ce mummuna kawai za a dibga.

” Babbat matsalar mu ita ce Najeriya na cikin sahun kasashe masu hako danyen man fetur da tsadar gaske. Ana kashe dala 15 zuwa 17 wajen hako kowace gangar danyen mai daya tal.

“To kenan idan har farashi ya fadi warwas daga dala 32 ko 30 zuwa dala 22, ai ba ka ma bukatar jiran sai wani malamin duba ya shaida maka cewa asara ka ke tabkawa idan ka ci gaba da hako danyen mai.

“Kasashen irin su Saudiyya da Iraq duk za su iya ci gaba da hako danyen mai, ko da ya kara karyewa da dala 8, Saudi za ta iya hakowa ta ci riba.

“Iraq za ta iya hakowa kuma ta ci riba, ko da ya kara raguwa da dala 5. Saboda su duk ba su kashe makudan kudade wajen hako danyen mai, kamar yadda kasashe irin Najeriya ke kashewa.”

Kyari ya danganta wannan gagarimar matsala ce da annobar cutar Coronavirus da kuma takun-sakar yakin danyen man fetur da ake yi tsakanin kasar Rasha da kuma Saudi Arabiya.

Ya zuwa yau dai ba a sani ba, ko Najeriya ta fara tunanin dakatar da hako danyen mai din, ganin cewa farashin sa bai kai dala 25 ba.

Yanzu dai tunda farashin danyen mai ya fado zuwa dala 18 kowace ganga daya, zai yi wahala NNPC ta ci gaba da dawainiyar kula da hako danyen mai akan dala 17 ladar aikin hako kowace ganga.

Share.

game da Author