CORONAVIRUS: Mutum na biyu ya mutu a Najeriya – Minista

0

Ministan Kiwon Lafiya Osagie Ehanire ya bayyana wa kwamitin shugaban kasa kan coronavirus cewa a ranar Litinin wani da ke fama da cutar coronavirus ya rasu.

Wannan shine mutum na biyu da ya rasu a dalilin kamuwa da wannan cuta ta coronavirus.

Sai dai kuma ministan ya ce dama can wannan mara lafiya yana da wasu manyan cututtuka da ayke fama dasu kafin cutar ta afka masa,

” Har yanzu dai mutum uku ne suka warka daha wannan cuta a Najeriya, biyu sun rasu.

Idan aba a manta ba mutum na farko wadda tsohon ma’aikacin PPMC ne ya rasu bayan dawowarsa daga kasar Birtaniya da ake duba shi.

A najeriya cutar ta bayyana a jihohi kusan bakwai Sannan akwai manyan jami’an gwamnati da suma suna kwance ana duba bayan sun kamu da cutar.

Ciki akwai gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai da gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed.

Haka kuma akwai shugaban ma’aikatn fadar shugaban Kasa, Abba Kyari da shima yana kwance ana duba shi.

Akalla akwa mutane 111 yanzu da suka kamu da cutar a Najeriya sannan kuma ana ci gaba da duba wasu da dama da ake zargin sun kamu da cutar,

Attajirai da manyan bankunanan Najeriya na ta mika tallafin biliyoyin naira do wannan yaki da gwamnati ta sa a gaba.

Share.

game da Author