Hukumar NCDC ta bayyana cewa an samu Karin mutane 8 da suka kamu da cutar coronavirus a Najeriya a ranar Asabar.
Mutum 7 a Legas daya a jihar Benuwai.
Wannan shine karo na farko da aka samu wani daga jihar Benuwai ya kamu da cutar.
Yanzu akalla mutum 89 kenan suka kamu a Najeriya.
Jihar Legas na da mutum 59 da suka kamu da cutar zuwa yanzu, Abuja 14, Ogun 3, Oyo 3, Enugu, Edo da Bauchi, bibbiyu, Ekiti, Benuwai, Osun, Ribas daidai.
Za a iya samun Karin yawan mutanen da suka kamu da cutar a kasar nan ganin yadda gwamnati ta maida hankali wajen gano wadanda suka yi cudanya da wadanda suka kamu.
Attajirai da manyan bankunan Najeriya suna ta aikawa da gudunmawarsu ga hukumar NCDC, domin tallafa mata wajen aikin kau da cutar da take yi.
Hatta ministocin Najeriya sun bada gudunmawar rabin albashin su na watan Maris ga wannan hukumar.
A duniya kuma mutane sama da 600,000 aka tabbatar sun kamu sannan akalla 27,000 sun mutu.
Kasar Spain da Italiya ke kan gaba wajen yawan mutanen da ke mutuwa a kullum a dalilin kamuwa da cutar.
Sama da Mutane 500 suke mutuwa a kullum daga wadannan kasashe.
Ita ma kasar Amurka ta bi sawun kasashen da cutar ta dabaibaye.
Yanzu ta fi kowacce kasa a duniya yawan wadanda suka kamu da cutar, sannan akwai sama da mutum 1000 da suka kamu.
A Nahiyar Afrika, har yanzu akwai kasashen da basu kamu da cutar ba. Sai dai kasashe kamar su Afrika ta Kudu da wasu manyan kasashen nahiyar sun fada tsundum ciki.
Kasashen Bostwana, Burundi, Lesotho, Malawi, da wasu tsiraru basu samu bayyanan cutar a kasashen su ba. Sai dai sun dauki matakan kare mutanen su.
Discussion about this post