Hukumar NCDC ta sanar cewa wasu mutum hudu sun kamu da cutar coronavirus a Najeriya ranar Litinin.
Hukumar ta fadi haka ne ranar Talata da misalin karfe 11:15 na safe.
3 a jihar Osun, 1 a jihar Ogun.
A yanzu dai mutum 135 ne ke dauke da cutar, 8 sun warke, biyu sun mutu.
Legas – 81
FCT – 25
Ogun – 5
Enugu – 2
Ekiti – 1
Oyo – 8
Edo – 2
Bauchi – 2
Osun – 4
Ribas – 1
Benuwai – 1
Kaduna – 3
Za a iya samun Karin yawan mutanen da suka kamu da cutar a kasar nan ganin yadda gwamnati ta maida hankali wajen gano wadanda suka yi cudanya da wadanda suka kamu.
A jawabin da shugaban Kasa Muhammadu Buhari yayi wa ‘yan Najeriya ranar lahadi ya ce gwamnati ta saka dokar garkame garin Abuja da Legas na makonni biyu har sai an kammala yin gwajin wadanda ake zargin sun kamu da cutar.
Attajirai da manyan bankunan Najeriya suna ta aikawa da gudunmawarsu ga hukumar NCDC, domin tallafa mata wajen aikin kau da cutar da take yi.
Hatta ministocin Najeriya sun bada gudunmawar rabin albashin su na watan Maris ga wannan hukumar