Cutar Coronavirus da ta bullo a kasar Chana a watan Disambat 2019 ta kama mutane 2,400 a kasar Jamus.
Gwamnatin kasar ta bayyana cewa ta samu yawan mutane haka ne a jihohi 16 dake kasar.
Bisa ga rahotan jihar North Rhine Westphalia da ta fi yawan mutane a kasar cutar ta kama mutane sama da 900, a jihar Bavaria mutane 500 sannan Wuerttemberg mutane 330 na dauke da cutar.
A takaice dai a kasar mutane biyar ne suka mutu sannan mutum daya dan kasar ya mutu a kasar Masar.
Idan ba a manta ba a watan Fabrairu 2020 ne Ma’aikatar Lafiya ta kasar Jamus ta bayyana barkewar cutar coronavirus a kasar, inda ta ce a dan kankanin lokaci mutum goma ya kamu.
Cikin sanarwar da mahukuntan kasar suka bayyana sun ce yanzu haka an fantsama nema da gwajin gano duk wani mai dauke da cutar, ko kuma mai alamun kamuwa da ita.