Kungiyar kiwon lafiya ta duniya (WHO) ta bayyana cewa a cikin awa 24 mutane 17 sun mutu a dalilin kamuwa da cutar Coronavirus a Afrika.
Zuwa yanzu mutane 633 na dauke da cutar a Afrika, mutane 17 sun mutu.
Har yanzu kasar Masar ne kasar da ta fi fama da yaduwar cutar a Afrika da a yanzu haka mutane 210 sun kamu da cutar.
Daga nan kuma sai kasar Afrika ta Kudu inda mutane 116 sun kamu da cutar sannan kasar Algeria dake da mutum 75 da suka kamu da cutar.
Shugaban WHO Tedros Ghebreyesus ya yi kira ga kasashen duniya da su karfafa matakan hana yaduwar cutar duk da cewa masana kimiya na gab da gano maganin cutar.
Ghebreyesus kungiyar za ta ci gaba da tallafa wa kasashen da basu da karfin samun kayan gwajin cutar.
Idan ba a manta ba a ranar Laraba ne WHO ta sanar cewa mutane 400 sun kamu da cutar a kasashen Afrika inda 41 daga cikin su sun warke.
Sannan a Najeriya mutane 8 ne ke dauke da cutar zuwa yanzu haka.
Kwayoyin cutar CoronaVirus na daga cikin kwayoyin cutar dake sa a kamu da mura wanda idan yayi tsanani akan yi fama da matsalar cutar dake hana numfashi yadda ya kamata da ake kira (Middle East Respiratory Syndrome (MERS-CoV), da kuma cutar tsanannin mura da kan toshe makogoro.
Alamun kamuwa da cutar sun hada da matsala a kafofin wucewar iska a makogoro wato numfashi, yawan zazzabi, tsananin tari, da ciwo a makogoro.
Idan abin yayi tsanani, ya kan kai ga shakar iska ma ya gagara, sannan a samu matsalar sanyin hakarkari wato ‘Nimoniya’, kuma idan har ya yi tsanani matuka kodar mutum kan daina aiki kwata-kwata.
Za a iya kaucewa kamuwa da wannan cuta ta hanyar, yawaita wanke hannaye da ruwa da sabulu, sannan a rika rufe hanci da baki idan za ayi atishawa kuma a rika wankewa da dafa nama sosai ya nuna tubus kafin a ci da kwai.
A rika nisanta ko kuma zama kusa da wanda ya nuna alamun rashin lafiya musamman irin wadanda a ka lissafa a sama sannan a gaggauta zuwa asibiti da neman magani idan ba a da lafiya.