Rahotannin kungiyar kiwon lafiya ta duniya WHO ya nuna cewa mutane 114,151 ne suka kamu da cutar cioronavirus, daga ciki 4,012 sun mutu a kasashe 105 a duniya.
Cutar dai ta ci gaba da yaduwa zuwa kasashen duniya inda hakan ya sa wasu kasashen daukan tsauraran matakai domin hana yaduwar cutar.
Tun daga watan Disamba zuwa yanzu ba a iya gano maganin cutar ba sannan cutar ta yi wa wasu kasashen kamun farad daya duk da matakan hana yaduwar cutar da suke dauka.
KASAR BIRTANIYA
Kamar yadda BBC ta rawaito ranar Laraba ta ce ministan kiwon lafiyar kasar ta kasar Britaniya Nadine Dorries ta kamu da cutar Coronavirus.
A yanzu dai Nadine na killace a gidanta inda a nan take samun kula.
Gwamnatin kasar ta ce ta fara gudanar da bincike domin gano ko akwai wadanda suka kamu da cutar a dalilin yin mu’amula da Nadine.
Ita kuwa Nadine ta ce tana fargaban mahafiyarta ta kamu da cutar domin a ranar Talata mahaifiyar na tari.
Mutane 382 ne ke dauke da cutar a kasar UK inda daga ciki mutane shida suka mutu.
KASAR AMURKA
Rahotannin jami’ar John Hopkins da aka gabatar ranar Talata ya nuna cewa mutane sama da 1000 sun kamu da coronavirus a kasar.
Bisa a rahotan mutane sama da 31 sun mutu a dalilin kamuwa da cutar daga jihohi 38 da Wahinton DC a kasar.
KASAR ITALIYA
A ranar Talata gwamnatin Kasar Italiya ta sanar cewa mutane 168 sun rasu cikin awa 24 a kasar.
Mahukunta sun ce mutane 631 sun rasu tun barkewar cutar sannan sama da mutane 10,000 sun kamu da cutar.
Wannan matsala ya razana gwamnatin kasar da mutanen kasar inda an dakatar da ayyuka da dama har da makaranta.
Wannan shine mafi yawan rayuka da aka rasa bayan kasar Chana da cutar ta samu asali daga.
KASAR JAMUS
Ma’aikatar Lafiya ta kasar Jamus ta bayyana barkewar cutar coronavirus a kasar, inda ta ce a dan kankanin lokaci mutum goma ya kamu.
Ministan Lafiyar Jamus, Jens Spahn ya bayyana a birnin Berlin cewa yanzu haka an fantsama nema da gwajin gano duk wani mai dauke da cutar, ko kuma mai alamun kamuwa da ita.
KASASHEN GABAS TA TSAKIYA
KASAR SAUDIYYA
Cutar Coronavirus na cigaba da yaduwa a kasashen gabas ta tsakiya musamman kasashen Kuwait, Qatar, Saudiyya da Egypt.
Ma’aikatar Kiwon Lafiya ta Kasar Saudiyya ta bayyana cewa bayan karin mutum biyar da aka samu sun kamu da cutar a kasar, yanzu an tabbatar da mutane 20 kenan da ke dauke da ita a kasar.
Cikin mutane biyar din da aka gano yau, hudu yan kasa ne. Uku daga cikin su sun dawo daga kasar Iran da Iraqi ne daya daga kasar Masar.
Saudiyya ta dakatar da fita da shigowan jirage daga kasashe 14 da suka hada da
United Arab Emirates (UAE), Egypt, Kuwait, Bahrain, Iraq, Lebanon, Syria, South Korea, Italy, Oman, France, Germany, Turkey da Spain.
Bayan haka kuma ta sanar da rufe makarantun kasar daga ranar litini.
Sannan kuma za a rika rufe masallatan Makka da na Madina bayan sallar Ishha’i, kuma gwamnati ta dakatar yin Umrah.
KUWAIT
Kasar Kiwait ta sanar da sabbin wasu mutum hudu da suka kama da ya kara ywan adadin mutanen da ke dauke da cutar a kasar zuwa 69.
QATAR
Akalla mutane 18 ne aka tabbatar sun kamu da cutar a kasar Qatar.
EGYPT
Kasar Masar wacce ita kasa ta farko a Nahiyar Afrika da aka bayyana shigar cutar, zuwa yanzu akalla mutane 59 ne ke dauke da cutar.
Firaye Ministan Kasar Mostafa Madbouli ya bayyana cewa an saka dokar hana taro da gangami a fadin kasar zuwa yanzu don kada a yada cutar.
NAHIYAR AFRIKA
Coronavirus ta yadu zuwa kasashe 11 a Afrika inda mutane kusan 100 sun kamu da cutar.
Wadannan kasashe sun hada da Jamhuriyyar Kongo, Algeria, Burkina Faso, Afrika ta kudu, Senegal, Tunisia, Togo, Masar, Kamaru, Najeriya da Morocco.
BUKINA FASO
Ministan kiwon lafiya ta kasar Bukina Faso Claudine Lougue ya sanar cewa mutane biyu sun kamu da cutar Coronavirus a kasar.
Lougue y ace an gano wannan cuta ne a jikin wasu ma’aurata mata da miji sannan an killace su tare da wani a dake zargin ya kamu da cutar a dalilin yin mu’amula da ma’auratan a asibitin dake Ouagadougou.
Daga Daga nan kuma mutum daya ya sake mutuwa a dalilin kamuwa da cutar a kasar Morocco.
AFRIKA TA KUDU.
An samu karin mutane shida da suka kamu da coronavirus a kasar Afrika ta Kudu.
Hukumar hana yaduwar cututtuka ta kasar ta sanar da haka ranar Laraba inda ta kara da cewa jimmlar mutanen da suka kamu da cutar a kasar ya kai 13.
Hukumar ta ce wasu na kwance a asibiti sannan wadanda cutar bai yi tsanani ba a jikinsu na killace a gidajen su.
KASAR KAMARU.
Kasar Kamaru ta killace mutum na farko da aka yi wa gwaji aka gano ya kamu da cutar coronavirus.
Mutumin wanda dan asalin kasar Fransa ya tsallako kasar ne inda na’urar gwaji ya nuna yana dauke da cutar.
Ministan kiwon lafiyar kasar, Malachie Manaouda ya bayyana cewa tuni dai har an killace wannan bafaranse a babban asibiti dake Yawonde.
NAJERIYA
Hukumar NCDC ta bayyana cewa an gano wani dan Najeriya da ba bako ba ya kamu da cutar coronavirus.
An killace wannan mutum a wani asibiti ana duba shi a jihar Ondo.
Shi dai wannan mara lafiyan yana daga cikin wadanda suka yi mu’a’mula da baItaliyan da ya shigo wa Najeriya da wannan cuta.
KASAR MASAR
An samu mutum na farko da ya fara mutuwa a nahiyar Afrika a kasar Masar wato Egypt.
Wanda ya rasu din dan asalin kasar Jamus ne da aka killace a wani asibiti dake kasar mai shekaru 60.
Ministan Lafiyan kasar Masar ya bayyana cewa wannan mutum ya shigo kasar Masar ne a jirgin ruwa na yawon bude ido.
Kafin wannan jirgin yawon bude Ido ya iso kasar Masar, mutane uku ne kacal aka tabbatar sun kamu da cutar. Zuwan wannan jirgin yasa an samu karin wasu da dama, da ya kai mutane 55 a kasar. 19 daga cikin su baki ne
JAMHURIYYAR KONGO.
Ministan kiwon lafiya ta kasa Kongo Eteni Longondo ya bayyana cewa an gano coronavirus a jikin mutum daya a kasan.
Longondo y ace mutumin ya yi tafiya zuwa kasar Faransa inda bayan ‘yan kawanki da dawowa ya fara rashin lafiya.
Ya ce an killace mutumin a asibiti sannan har ya fara samun sauki.
Wannan shine ne karon farko da wani dan kasar ke kamuwa da cutar.
Discussion about this post