CORONAVIRUS: Matafiyi ya tsorata mutane a filin jirgin Aminu Kano

0

Mutane a filin jirgin saman Aminu Kano sun firgita bayan jirgin Air Peace daga Legas ya sauka a filin jirgin kuma yana dauke da wani yaro mara lafiya a cikin sa.

Mutane sun firgita cewa wannan yaro yana dauke da cutar coronavirus ne, a dalilin haka lallai sai dai jirgin ya koma can Legas ko kuma ya garzaya Gwagwalada inda ake kula da wadanda ke dauke da cutar.

Sai dai tun a farko matukin jirgin ya hana kowa sauka domin fargaba da rudani da mutane suka fada a lokacin.

Kakakin gwamnan jihar Kano Tanko Yakasai ya bayyana cewa ba cutar coronavirus bane ya ke dauke da shi wannan matafiyi.

Ya ce wannan matashi ya rude ne a dalilin hawan jirgin sama da yayi a karon farko kenan.

Mahukunta sunce tuni har anyi wa wannan matafiyi gwajin cutar, kuma an samu bashi da ita.

Cibiyar Kula da Yaduwar Cututtuka ta Najeriya, NCDC, ta kara bayyana cewa an samu karuwar masu dauke da cutar Coronavirus a Najeriya, daga mutum 35 da ta bayyana a ranar Talata, zuwa mutum 42.

Sanarwar da Cibiyar ta buga a shafin tattara bayanan ta da kuma shafin ta Twitter a safiyar Talata din nan, NCDC ta ce an kara samun wadanda suka kamu da cutar har mutum hudu a ranar Litinin.

Cikin sanarwar, NCDC ta tantance cewa mutum 28 daga kasar waje suka shigo da cutar, domin dukkan su sun fita waje a cikin makonni biyu da suka gabata.

An kara samun mutum uku a Lagos da kuma mutum daya a Abuja.

Idan ba a manta ba, PREMIUM TIMES ta buga labari a ranar Litinin cewa Najeriya ta tabbatar da karin mutum biyar masu dauke da cutar Coronavirus.

Cibiyar Kula da Cututtuka ta Kasa ce ta bayyana haka a jiya Litinin, a shafin ta na Twitter cewa an samu karin mutanen biyar ne a Abuja mutum biyu, Lagos mutum biyu said kuma da kuma Jihar Edo inda aka samu mutum daya.

An tabbatar da cewa karin mutane biyu da aka samu daga Abuja, su na daga cikin matafiyan da suka dawo daga Ingila kwanan nan, lokacin da cutar ta yi kamari a can.

Ana jin cewa dan Atiku Abubakar da ya kamu daga cutar, na daya daga cikin wadanda ake cewa sun kamu a Abuja din.

Share.

game da Author