Rahotanni da a ka fitar a daren Lahadi cutar coronavirus ya zama annoban gasket a kasar Italiya.
Akalla mutane 133 ne suka rasu cikin awa 24 a kasar inda aka samu Karin wadanda suka kamu a wannan awowi har Sama da 2000.
Wannan marsala ya razana gwamnatin kasar da mutanen kasar inda an dakatar da ayyuka da dama har da makaranta.
A kasar Iran ma, an sanar da Hana fitowa salloli da sallar Juma’a da duk wasu tarorruka da zai Tara jama’a.
Kasar Italiya ce ta uku da cutar ta fi yaduwa.
Baya ga kasar Chana da Koriya Ta Kudu da sune ke kan gaba sai kasar Italiya.
Hatta wasan kwallon kafa an dage su, wadanda za a buga su kuma, za a buga ne babu yan kallo.
Akalla Sama da mutum 197 suka rasu a kasar Italiya zuwa yanzu. Haka itama kasar Faransa cutar ya ci gaba da yaduwa da ya kai ga an dage wasan kwallon kafa daya da ya kamata a buga shi yau.
Mutane 49 suka rasu cikin awa 24 a kasar. Sannan akwai wasu 4,600 da suka kamu.
Mutane sama da 98,000 suka kamu da a duniya yanzu. Sannan sama da 3000 sun rasu zuwa yanzu.
Hukumar Kula da Lafiya da ke karkashin Majalisar Dinkin Duniya, ta bada sanarwar cewa masana daban-daban na duniya, sun fantsama kirkiro sinadaran magance cutar Conronavirus.
WHO ta ce har ma wasu masu aikin kirkirar magungunan sun kai ga matakan yin gwaje-gwajen gane tabbaci da kuma ingancin kwayoyin maganin.
Da ya ke har yau babu takamaimen maganin cutar, ya zuwa Asabar ta yadu a kasashe har 49, kuma sama da mutum 2,000 ne cutar ta kashe daga Disamba zuwa karshen watan Maris.
Kasashen Denmark, Estonia, Lithuania, Netherlands da Najeriya duk sun bayyana an kamu da cutar daga kasar Italy a cikin kasashen su.
Ita ma Iran kamar yadda jami’in WHO mai suna Ghebreyesus ya bayyana, mutum 92 daga cikin daruruwan da suka kamu, duk daga waje aka shigar musu da ita.
Tun bayan bullar cutar ce Hukumar Lafiya ta Majalisar Dunkin Duniya (WHO) ta hada kai da Chana, su na hakilon nazarin ainihin yadda cutar ke shiga dan Adam, daga inda can ne asalin ta da kuma irin yadda ta ke mamayewar jiki da kuma irin illar da take yi.
Tun bayan barkewar cutar ne WHO ke ta kokarin wayar da kan kasashen da ta bulla da inda ba ta bulla ba, wajen sanar da su hanyoyin bi domin kauce wa wannan cuta da ta zama ruwan-dare cikin watanni uku.
WHO ta ce ta na wannan kokarin ne kafin jiran magungunan da masana suka dukufa binciken samarwa da kirkirowa.