Gwamnatin kasar Italiya ta sanar da rufe dukka ma’aikatun gwamnati, makarantu, kasuwanni, filayen wasanni, manyan shaguna da dai sauransu a dalilin annobar cutar coronavirus.
Italiya ita ce kasa ta uku cikin jerin kasashen da cutar ta yi wa kamun farad-daya.
A kusan kullum sai mutane da dama sun mutu wasu kuma sun kamu da wannan cuta ta coronavirus.
Gwamnatin kasar ta ce dole a maido da hankali kacokan wajen ganin an kawo karshen wannan matsala na ci gaba da yaduwar cutar a kasar.
A dalilin haka ta sanar da doka hana fita da shida da walwala a kasar daga yanzu.
Asibitoci a kasar duk sun cika fam da marasa lafiya sannan an fara karancin su.
Sai dai dokar bai hana zuwa kasuwa maza-maza ba don siyan abinci da kuma abubuwan da ake bukata.
A Najeriya mutum biyu ne kawai suka kamu tun bayan shi mata da cutar da wani dan kasar Italiya ya yi a watan Faburairu.