CORONAVIRUS: Karancin na’urar gwaji zai kawo cikas a Najeriya – Dr Tilde

0

Kwamishian ilimin jihar Bauchi Aliyu Tilde ya koka kan karancin na’urar gwajin cutar coronavirus a kasar nan yana mai cewa rashin isassu na iya kawo matsala a kasar ganin yadda ake ta samun karuwar cutar a fadin kasar nan.

Tilde ya fadi haka ne ranar Laraba bayan neman ayi masa gwajin cutar kuma ba a samu an yi masa aba a asibiti a jihar saboda rashin kayan aiki.

Ya je asibiti ne tun bayan da ya samu labarin cewa gwamnan jihar Muhammed Bala ya kamu da cutar kuma ya tuna sun yi mua’amula tare da gwamnan a yan kwanakinnan.

“Ina killace dai a gida na kuma bana jin alamun ciwon komai a jiki na amma ko da na je asibiti ban samu daman yin gwaji ba saboda babu kayan aiki. Amma zan koma zuwa gobe.

ANA BUKATAN KARIN KAYAN GWAJI

Tilde ya yi kira ga gwamnati ta karo kayan gwajin cutar domin gwaji na daga cikin hanyoyin wajen dakile cutar.

Ya kuma yi kira ga gwamnati da ta kara yawan wuraren yin gwajin cutar a yankin Arewa.

Tilde y ace a kasar nan wuraren yin gwajin cutar biyar ne, Abuja, Legas, Ondo da jihar Edo.

Tilde yace idan da zai yiwu gwamnati ta bude wuraren gwajin wannan cutar a duk kananan hukumomin kasar nan.

Ya ce yana sa ran sakamakon gwajin zai nuna baya dauke da cutar.

Mutane 46 ne ke dauje da cutar a kasar nan inda 30 daga cikinsu sun shigo kasar nan daga kasashen waje da cutar ta barke

Hanyoyi 10 da za a kiyaye domin kare kai daga CORONAVIRUS

1 – A rika Wanke hannuwa da sabulu a duk lokacin da aka dan wataya ko kuma aka yi tabe-taben abubuwa. Ko bako Kayi ka bashi dama ya wanke hannu kafin ku fara mu’amala.

2 – Ku rufe hanci da bakinku lokacin da kuke yin atishawa da gefen Hannu amma ba da tafin hannu ba. Idan kun shafi bakunan ku toh, ku wanke hannu maza-maza.

3 – A daina taba idanuwa da hannaye ko kuma hanci da baki. Ka du rika yawan shafa fuskokinku da hannaye. Idana an yi haka a gaggauta wanke hannaye.

4 – A nisanci duk wani da bashi da lafiya, musamman mai yin Mura da tari. Ko zazzabi ne yake yi a nisanta da shi sannan a bashi magani da wuri. Idan abin ya faskara a gaggauta kaishi asibiti domin a duba shi.

5 – A kula da yara sannan a rika tsaftace muhalli.

6 – A rika gaisawa da juna nesa-nesa

7 – Idan kayi bako daga kasar waje, kada a kusance shi koda dan uwana ne sai ya killace kan sa na tsawon makonni biyu.

8 – A rika Karantar da yara yadda za su kiyaye koda an aike su a waje.

9 – A yawaita cin abinci masu gina jiki, shan ruwa da motsa jiki.

10 – A yawaita yin addu’a da sadaka.

Share.

game da Author