CORONAVIRUS: Jihohin Legas da Kwara sun rufe makarantu

0

Gwamnatin jihar Kwara ta sanar da rufe duka makarantun jihar domin dakile yaduwar cutar coronavirus da ya fara yaduwa a kasar nan.

Babban sakataren yada labaran gwamnan jihar, Rafiu Ajakaye, ya sanar da haka ranar Alhamis.

Ajakaye yace za a rufe makarantun ne daga ranar Litini 23 ga watan Maris.

JIHAR LEGAS

Itama Gwamnatin jihar Legas ta sanar cewa makarantun gwamnati da na kudi a jihar za su tafi hutu daga ranar 23 ga watan Maris 2020.

Kwamishinan yada labarai Gbenga Omotosho ya sanar da haka inda ya kara da cewa gwamnati ta yi haka ne domin kare yara da malaman makarantun kamuwa da cutar coronavirus.

Hana tarurrukan mutane sama da 50 na cikin wasu matakan hana yaduwar cutar da gwamnatin jihar ta dauka.

Sannan a ranar Laraba an dakatar da wasannin kwallon kafa na kwararru da ake yi a kasar nan.

Idan ba a manta ba a ranar Laraba ne kungiyar gwamnonin yankin Arewa maso yammacin kasar nan suka yanke hukuncin a rufe makarantu na yankin zuwa kwanaki 30 masu zuwa.

Kungiyar ta ce daukan matakan dakile yaduwar coronavirus a yankin ya zama dole duk da cewa cutar ba ta bullo a yankin ba sannan sakamakon gwajin cutar da aka yi wa wasu mutane a yankin da ake zargin sun kamu da cutar ya nuna basu dauke da ita.

Za a rufe makarantun daga ranar Litini 23 ga watan Maris 2020 na tsawon kwanaki 30.

Ma’aikatar kiwon lafiya ta sanar cewa mutane 8 sun kamu da coronavirus a kasar nan.

Bincike ya nuna cewa mafi yawan wadannan mutane na da tarihin tafiya zuwa kasashen Amurka da UK:

Kwayoyin cutar Corona Virus na daga cikin kwayoyin cutar dake sa a kamu da mura wanda idan yayi tsanani akan yi fama da matsalar cutar dake hana numfashi yadda ya kamata da ake kira (Middle East Respiratory Syndrome (MERS-CoV), da kuma cutar tsanannin mura da kan toshe makogoro.

Alamun kamuwa da cutar sun hada da matsala a kafofin wucewar iska a makogoro wato numfashi, yawan zazzabi, tsananin tari, da ciwo a makogoro.

Idan abin yayi tsanani, ya kan kai ga shakar iska ma ya gagara, sannan a samu matsalar sanyin hakarkari wato ‘Nimoniya’, kuma idan har ya yi tsanani matuka kodar mutum kan daina aiki kwata-kwata.

Za a iya kaucewa kamuwa da wannan cuta ta hanyar, yawaita wanke hannaye da ruwa da sabulu, sannan a rika rufe hanci da baki idan za ayi atishawa kuma a rika wankewa da dafa nama sosai ya nuna tubus kafin a ci da kwai.

A rika nisanta ko kuma zama kusa da wanda ya nuna alamun rashin lafiya musamman irin wadanda a ka lissafa a sama sannan a gaggauta zuwa asibiti da neman magani idan ba a da lafiya.

Cutar da ta samo asali a kasar Chana a watan Disemba 2019 ya kama mutane 80,849 sannan da dama sun mutu a kasar.

Coronavirus ta yaduwa zuwa wasu kasashen duniya inda mutane 157,208 sun kamu da cutar wasu 5,842 sun mutu a kasashen duniya 153.

A yanzu dai kasashen Italiya da Masar a Najiyar Afrika na cikin kasashen da wannan cutar ta yi wa kamun farad daya.

Share.

game da Author