Jihar Cross River ta bayyana cewa aikin rangadin sanar da al’umma a cikin garuruwa da kauyukan karkara ya kankama, dangane da matakan kauce wa kamuwa da cutar CORONAVIRUS.
Kwamishinar Lafiya ta Jihar Cross River, Betta Udu ce ta sanar da cewa jihar ta bazama ta na amfani da maishela su na sanarwa a lunguna daban-daban da kuma cikin coci-coci a fadin jihar.
“Mu na amfani da masu shela, sannan kuma mun gana da shugabannin coci-coci, wadanda mu ka sanar da Jami’an Yada Labarai na Kananan Hukumomi za su rika aiki tare ko sanarwa a cikin coci-coci na jihar nan, domin wayar da kai.
Kwamishina Betta ta ce wannan mataki ne mafi sauki na gargajiya wanda sakonnin daukar matakan kariya daga kamuwa da cutar ke isa ga jama’a cikin gaggawa.
Ta ce za a rika yin bayanai da yarukan kowace al’ummar da ke zaune a wani yanki, sannan kuma za a rika amfani da Turancin gargaliyya, wato ‘pidgin English.’
“Sakon dai kai-tsaye shi ne: duk wanda ka ga ya na mura mai karfi, ya na tari, ya na atishawa, kuma ka ke da tabbacin cewa ya dawo ko ya zo ne kwanan nan daga wata kasar da cutar ta bulla, to ka gaggauta kai rahoto, kuma ka yi kaffa-kaffa da kusantuwa da shi.”
Ta ce an kebe wurin killace masu cutar ko wadanda ake zargin sun kamu a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Calabar.
Har yau dai tun bayan dan kasar Italy da aka samu da cutar a Lagos a cikin makon jiya, har yau ba a sake samun wani da cutar a cikin Najeriya ba.
Discussion about this post