Kungiyar gwamnonin Arewa maso Yammacin Najeriya na yunkurin dakatar da sallolin jam’i da sallar Juma’a a masallatai domin hana yaduwar cutar coronavirus a yankin.
Arewa maso Yammacin kasar nan yanki ne da da musulmai suka fi yawa inda a kullum suke taruwa a masallatai suna sallolin jam’i sau biyar a rana.
Haka kuma ranar Juma’a.
Gwamnan jihar Jigawa Muhammad Badarau ya sanar da haka a hira da yayi da BBC Hausa ranar Alhamis.
Badarau ya ce kungiyar za ta tattauna da sarkin Musulmi Sa’ad Abubakar domin ganin yadda za a iya dakatar da yin sallah a masallatai.
Sannan kuma da kirkiro hanyoyi domin wayar wa mutane kai game da cutar
RASHIN HANA TARURRUKAN ADDINI A KASAR NAN
Idan ba a manta ba a ranar 17 ga atan Maris ne mahukuntan kasar Saudiyya suka sanar da dakatar da yin sallolin jam’i da sallar Juma’a a duka masallatan kasar domin dakile yaduwar cutar coronavirus da yake yaduwa kamar wutar daji a kasashen duniya.
Gwamnati ta bayyana cewa wannan doka bai shafi masallatan Makka da Madina ba.
Sannan a ranar Laraba gwamnonin yankin Arewa Maso Yammacin kasar nan sun yanke hukuncin rufe makarantu na yankin zuwa kwanaki 30 masu zuwa.
Daukan matakan dakile yaduwar coronavirus a yankin ya zama dole duk da cewa cutar ba ta bullo a yankin ba sannan sakamakon gwajin cutar da aka yi wa wasu mutane a yankin da ake zargin sun kamu da cutar ya nuna basu dauke da ita.
Za a rufe makarantun daga ranar Litini 23 ga watan Maris 2020 na tsawon kwanaki 30.
Daga nan kuma a ranar Talata gwamnati ta hana jami’an ta yin tafiya zuwa kasanshen waje sannan a ranar Laraba aka hana jiragen wasu kasashe 13 daga sauka a kasar nan.
Gwamnati ta hana taron kwallon kafa da za a yi a kasan sannan ta rufe duk sansanonin horas da dalibai na hukumar NYSC dake kasar nan.
Gwamnatin jihar Legas ta hana taron mutane sama da 50 kuma za a rufe duk makarantun dake jihar sannan jihar Kwara ta rufe makarantun jihar domin kare mutane daga kamuwa da cutar.
Duk da wadannan matakan hana yaduwar cutar da gwamnati ta dauka babu inda ta fito ga da ga domin hana taron adini a kasar nan.
Shugaban cocin RCCG ne kadai ya yi kira ga mambobin sa da su guji taruwa sama da 50 a coci domin guje wa kamuwa da cutar sannan da yin biyayya da umurnin gwamnatin jihar Legas.
Kwayoyin cutar Corona Virus na daga cikin kwayoyin cutar dake sa a kamu da mura wanda idan yayi tsanani akan yi fama da matsalar cutar dake hana numfashi yadda ya kamata da ake kira (Middle East Respiratory Syndrome (MERS-CoV), da kuma cutar tsanannin mura da kan toshe makogoro.
Alamun kamuwa da cutar sun hada da matsala a kafofin wucewar iska a makogoro wato numfashi, yawan zazzabi, tsananin tari, da ciwo a makogoro.
Idan abin yayi tsanani, ya kan kai ga shakar iska ma ya gagara, sannan a samu matsalar sanyin hakarkari wato ‘Nimoniya’, kuma idan har ya yi tsanani matuka kodar mutum kan daina aiki kwata-kwata.
Za a iya kaucewa kamuwa da wannan cuta ta hanyar, yawaita wanke hannaye da ruwa da sabulu, sannan a rika rufe hanci da baki idan za ayi atishawa kuma a rika wankewa da dafa nama sosai ya nuna tubus kafin a ci da kwai.
A rika nisanta ko kuma zama kusa da wanda ya nuna alamun rashin lafiya musamman irin wadanda a ka lissafa a sama sannan a gaggauta zuwa asibiti da neman magani idan ba a da lafiya.
Cutar da ta samo asali a kasar Chana a watan Disamba 2019 ya kama mutane 80,849 sannan da dama sun mutu a kasar.
Coronavirus ta yaduwa zuwa wasu kasashen duniya inda mutane 157,208 sun kamu da cutar wasu 5,842 sun mutu a kasashen duniya 153.
A yanzu dai mutane takwas na dauke da cutar a Najeriya sannan kasashen Italiya da Masar a Najiyar Afrika na cikin kasashen da wannan cutar ta yi wa kamun farad daya.