CORONAVIRUS: Gwamnatin Lagos ta umarci kashi 70% na ma’aikatan jihar su zauna a gida

0

Gwamnatin Jihar Legas ta umarci kashi 70% bisa 100% na ma’aikatan jihar da kada su fitar aiki, har tsawon kwanaki 14, tun daga ranar Litinin, 23 Ga Maris.

Wannan umarni ya shafi dukkan ma’aikatan jihar masu matakin albashi daga Level 1 zuwa Level 12, wadanda sun kunshi kashi 70% bisa 100% na ilahirin ma’aikatan gwamnatin jihar Lagos

Da ya ke karanta sanarwar, Gwamna Babajide Sanwo-Olu ya ce an dauki wannan matakin gaggawa ne, ganin yadda cutar Coronavirus ke kara ci gaba yaduwa a Lagos.

Ya ce wadannan rukunonin ma’aikata kowa ya zauna a gida, tsawon makonni biyu, domin a rage cinkoson jama’a.

Ya kara da cewa idan cutar ta nuna raguwa sosai, to za a kirawo ma’aikatan domin su ci gaba da ayyukan su.

Sai kuma gwamnan ya kada jami’an kula da lafiya, ma’aikatan kwasar shara, jami’an kashe gibara da sauran masu ayyukan agajin gaggawa su su zauna.

“Su babu su a cikin wadanda aka ce su zauna a gida.” Inji gwamnan.

A jihar Lagos ne aka fi kamuwa da Coronavirus a Najeriya, inda a cikin 30 da suka kamu, 19 duk a Lagos din suke.

Share.

game da Author