Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana kwashe dalibai har su 780 kuma ta maida su a jihohin su na asali.
Daliban su 780 dai su na karatu ne a makarantun sakandare daban-daban na Jihar Kano. An zabo su ne daga jihohi 17 a Arewacin Najeriya.
Kakakin Yada Labarai na Ma’aikatat Ilmi ta Jihar Kano, Muhammad Sanusi, ya ce an kwashe daliban ne aka maida jihohin da aka turo su, saboda tsoro da fargabar barkewar Coronavirus.
Ya ce shekaru talatin kenan a ba iron wannan tsari na turo yara dalibai zuwa Kano domin su saba da al’adun mutanen yankin, dabi’un su da kuma sanin addinin su.
Ya ce shiri ne da aka kirkiro shi domin kara hada kan ‘yan Najeriya mazauna yankunan da kabilu da dama.
Tuni dai aka rufe makarantu kasar nan, tun daga fitamare har zuwa jami’o’i, ganin yadda cutar ke kara yaduwa a kasar nan.
A jiya Lahadi kuma tsohon mataimakin ahugaban kasa, Atiku Abubakar, ya bada sanarwar dan sa ya kamu da cutar Coronavirus.
Ya ce tuni aka killace dan na sa a asibitin killace masu cutar Coronavirus da ke can a Gwagwalada, Abuja.