Ma’aikatar ilimin jihar Bauchi ta umarci duk makarantun Allo dake fadin jihar su maida yara Almajirai ga iyayen su maza-maza domin kaucewa yaduwar cutar coronavirus.
Kwamishinan ilimin jihar Dr Aliyu Tilde ya sanar da haka a takarda da ya fitar ranar Talata.
Tilde ya ce ” Dole a kare Almajirai daga wannan cutar kamar yadda aka kare yan makarantar boko. Almajirai na zuwa daga garuruwa dabam dabam kuma su koma garuruwansu bayan sun ci rani. Idan ciwo ya kama d’ayansu, nan da nan sauran almajirai za su kamu kuma ba wani isasshen tanadi na lafiya da ake da shi kan wannan cutar.”
Karanta sakon
BAYANIN GAMAGARI
Ma’aikatar Ilimi ta Jaha ta lura cewa har yanzu akwai makarantun Islamiyya da na allo da ke gudanar da karatu. Wannan ya sab’awa umarnin da gwamnati ta bayar game da rufe ilahirin makarantu don kauce wa yaduwar cutar koronabairus.
Dole a kare almajirai daga wannan cutar kamar yadda aka kare yan makarantar boko. Almajirai na zuwa daga garuruwa dabam dabam kuma su koma garuruwansu bayan sun ci rani. Kullum sai sun yi yawo a kwararo da gidaje don baran abinci. Wannan ya sa su cikin had’arin kamuwa da yad’a wannan cuta fiye da kowane jinsi na mutane a al’umma. Idan ciwo ya kama d’ayansu, nan da nan sauran almajirai za su kamu kuma ba wani isasshen tanadi na lafiya da ake da shi kan wannan cutar.
Don wannan Ma’ aikatar Ilimi take kira ga dukkan masu makarantun Islamiyya da na allo da su rufe su, su mai da almajiransu gida har sai an ga karshen wannan bala’i.
Duk makarantu da kosa-kosai na karshen mako na kowane irin karatu suma a rufe Su nan da nan.
Allah ya nuna mana sauki da karshen wannan annoba. Muna fata kafafen watsa labaru, musamman a rediyo, za su taimaka su yada wannan bayani a birni da kauye.
Daga
Dr. Aliyu U. Tilde
Komishina
Ma’aikatar Ilimi
Jahar Bauchi