Yayin da cutar Coronavurus ke kara yaduwa a manyan biranen biyu, gwamnatin tarayya ta yi kakkausan gargadi ga mazauna biranen Lagos da Abuja cewa a daina fita, kowa ya zauna cikin gidajen su.
Sakataten Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha ne ya yi wannan kakkausan gargadi a ranar Litinin, lokacin da ya ke karanta jawabin sa a wani taron manema labarai a Abuja.
“Mu na mika wannan kakkausan gargadi ga mazauna Lagos da kuma Abuja cewa a daina fita waje, a guji shiga cikin taron jama’a, ko ma wane irin taro ne. Fitar ma sai ta dole kawai za a yi, daga yau had zuwa lokacin da za a sake jin wani umarni daga gare mu.”
Sai dai kuma wannan gargadi ba oda ba ce gwamnati ta bayar. Hakan na nufin mutane za su iya fita su yi walwala a wasu wuraren kenan.
Sai dai kuma masana tattalin arziki na ganin cewa irin wannan umarni ba zai yi tasiri ba, a garuruwa kamar Lagos, inda kusan mutane milyan 19 duk sun dogara ne su fita yau domin samo abincin gobe.
Don haka zaman gida ga irin wadannan jama’a abu ne mawuyaci, musamman ganin cewa iya gwamnatin jiha da ta tarayya duk ba su yi wani tanajin saukake wa jama’a kuncin rayuwa ba a irin wannan mawuyacin yanayi na zaman gida.
PREMIUM TIMES ta buga labarin yadda a karshen makon da ya gabata, gwamnatin Jihar Lagos ta bada umarnin hana taron da ya wuce mutane 20. Sai dai kuma a wurare da yawa duk bijire wa umarnin aka yi, domin mashaya, gidajen rawa da sauran wuraren taron holewa da yawan gaske sun cika fal.
Sakataren Gwamnati Mustapha ya ce gwamnati na ci gaba da daukar kwararan matakan kara samar da cibiyoyin gwaji da kuma kayan gwajin da hanyoyin ganowa ko zakulo masu dauke da cutar.
Ya kuma sanar da kokarin ci gaba da yi wa jami’ai horo domin kokarun dakile cutar.
Daga nan ya bada sanarwar rufe kan iyakokin kasar nan na kasa, kwanaki bayan rufe manyan filayen jiragen saman kasar nan, tare da hana jirage daga kasashen da wannan cuta ta yi kamari sauka a Najeriya.
Sakataren ya kara jaddada matakan da Fadar Shugaban Kasa ta dauka, kuma ya yi kira ga jihohi su tabbatar su na tirsasa a bi duk wata dokar da aka kafa.
“Idan ta kama wannan Kwamitin Shugaban Kasa na Shirin Dakile Coronavirus ya ga akwai bukatar yin amfani da wani ginin hukuma, to zai sanar da gaggawa.
“Sannan idan akwai bukatar yi wa ma’aikatan Gwamnatin tarayya jawabi ko ba su wani umarni, to za a ji daga bakin Shugabar Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya.
Discussion about this post