CORONAVIRUS: Gidauniyar Dangote tallafawa Najeriya da gudunmawar Naira miliyan 200

0

Gidauniyar Aliko Dangote tallafawa wa gwamnatin Najeriya da gudunmawar Naira miliyan 200 domin inganta aiyukan hana yaduwar cutar Coronavirus a kasar nan.

Shugaban gidauniyar Zouera Youssoufou ta sanar da haka a wani takarda da aka raba wa manema labarai ranar Talata a Legas.

Youssoufou ta ce Daga cikin wadannan kudade za a yi amfani da Naira miliyan 124 domin tallafa wa asibitocin kula da masu fama da cutar dake kasar nan.

Ta kuma ce gidauniyar za a yi amfani da Naira miliyan 36 domin karfafa aiyukkan gudanar da bincike kan cutar sannan a yi amfani da Naira miliyan 48 domin horas da ma’aikatan kiwon lafiya da ma’aikatan sa kai hanyoyin dakile yaduwar cutar.

Idan ba a manta ba a lokacin da cutar Ebola ta bullo gidauniyar Dangote ta bada gudunmawar Naira biliyan daya domin dakile yaduwar cutar a Afrika.

Gidauniyar ta kuma tallafa wa gwamnatin Najeriya wajen inganta matakan hana yaduwar cutar a kasar nan.

Idan ba a manta ba a ranar 27 ga watan Fabrairu ne Ma’aikatar Lafiya ta kasa ta sanar cewa wani dan kasar Italy ya shigo Najeriya da cutar coronavirus daga kasar Italy.

Ma’aikatar ta bayyana cewa, wannan mutum dai ya shigo Najeriya ne daga kasar Italy inda bayan kwana daya da shigowa kasan ya fara rashin lafiya.

Daga nan sai aka kai shi asibiti inda aka gano cewa ya na dauke da cutar.

Coronavirus ta yadu zuwa kasashe 73 ban da kasar Chana sannan mutane 90,000 sun kamu da cutar inda daga ciki sama da 3,000 sun mutu.

Share.

game da Author