Gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya koka kan yadda mutane suka yi watsi da umarnin gwamnati na kada a rika yawace yawace, zirga-zirga da halartar tarukka domin dakile yaduwar cutar coronavirus amma suka yi wa umarnin kunnen uwar shegu.
Gwamna El-Rufai ya ce ko mutane su bi wannan umarni ko kuma a saka dokar garkame jihar gaba daya, ba fita ba shiga domin kare talakawa.
A jawabin da yayi ranar Litinin ya bayyana fushin sa matuka cewa lallai akwai jahilci da taurin kai ga mutane duk da ganin yadda kasashen duniya da Najeriya da kanta ke fama da wannan matsala na annobar coronavirus.
El-Rufa ya ce
1 – Daga ranar talata za a rufe kasuwannin jihar sai dai idan kayan abinci kake siyarwa ko kuma magani. Sannan gwamnati za ta yi wa kasuwannin feshi. kowa ya zauna a gida.
2 – Za mu tattaba an rufe ko wane irin makarata, ta Islamiyya ko Boko a fadin jihar. Kuma mun baza jami’an tsaro su tabbatar da an yi haka.
3 – Kowa ya tsaya a gida sai dai idan ya zama dole a fita.
4 – Haka kuma matafiya, suma an umarce su da su rage yin tafiye-tafiye idan ba ya zama dole ba. A dalilin haka muka sa aka dakatar da jigilar fasinja daga Abuja zuwa Kaduna.
5 – Mu na rokon wadanda suka dawo daga kasashen waje a ‘yan kwanakinnan su killace kansu maza-maza, idan suka ji ba dadi kuma su gaggauta garzayawa asibiti a duba su. ga lambar waya – 08025088304, 08032401473, 08035871662 and 08037808191.
6 – Da ga ranar Talata, gwamnati ta dakatar da duk wani ma’aikaci bai wuce mataki 12 ba da ya zauna a gida na tsawon wata daya.
7 – Ko wa ya zauna a gida babu fita ko kuma galantoyi a tituna. Idan ba haka ba kuwa za a saka dokar garkame jihar gaba daya.
A karshe gwamna El-Rufai ya ce wannan ba abinda za a rika wasa da shi bane. kowa yana ganin yadda kasashen duniya suke kokarin rurrufe ko-ina domin kauce wa wannan cuta. Ba zai yiwu gwamnati ta zuba ido ta bari saboda halin ko-in-kula da wasu ke yi ana samun matsala a jihar ba.
Duka abin da zaka yi sai kana da lafiya za aka iya yin shi saboda haka. Dole gwamnati ta tsaurara matakai matuka domin kiyaye jama’a.