Jihohi da dama sun kafa dokoki daban-daban da nufin aukar matakan hana yaduwar cutar Coronavirus a cikin jihohin su. Tsauraran matakan da wasu jihohin suka dauka, sun sha bamban da na wasu jihohin.
Wakilin mu da ya bi hanya a ranar Juma’a, daga Abuja zuwa Kano, ya yi nazarin abubuwa 10 suka sa ya ke tunanin cewa wadannan dokokin ba za su yi tasiri sosai ba.
1. Sanarwar hana shiga wasu jihohi daga rana kaza ga watan kaza, ta haifar da cunkoson jama’a zuwa wadannan jihohi, daga wasu jihohin. Misali, Kanawa da mutan Kaduna mazauna Abuja sun rika guduwa daga Abuja zuwa Kano da Kaduna.
A yanayin annoba kuwa, an fi so kowa ya zauna a inda ya ke. Domin ba a san wanda ke dauke da cutar ba. Watakila sai bayan an rufe hanya ta rika nunawa a cikin mutane.
2. Wakilin mu ya lura a Abuja da Lagos ne kadai cutar Coronavirus ta fi tayar wa jama’a hankali, sai kuma a soshiyal midiya. Domin da ka bar Abuja ka isa Zuba, kilomita 25 daga Abuja, za ka ga jama’a na ta hada-hada makil kamar jihar Neja ba ta sa sokar hana walwala a killace kowa ba.
3. A Kaduna an killace motoci, an hana su zirga-zirga zirga a cikin gari. Amma kuma yawancin mutane na zazzaune kofar gidaje da sauran wurare, ana ta tattauna halin da kasa ke ciki.
Da yawa hankalin na kan tunanin an hana su fita neman abinci. Wato ba su ma tunanin killace kan su a gida saboda Coronavirus.
4. An hana motoci zirga-zirga cikin Kaduna, amma motoci na wucewa ta gefen garin (by-pass), su na sauke fasinjoji, su kuma su na dannawa cikin gari.
5. Masallatan cikin birnin Kano da na garuruwan jihar sun gudanar da sallolin Juma’a, duk kuwa da rufe wuraren ibadu da kasashen duniya da Lagos da Kaduna su ka yi.
6. Talakawa da dama na ganin lallai maganin cutar Coronavirus na can a maaallaci, ta hanyar gudanar da addu’o’i. Dalili kenan ma wasu masallatan ke dan kara cika, kamar a lokacin sallar asubahi, bisa wani tsainkaye da wakilin mu ya yi a Kano.
7. Duk da Kano ta fi sauran jihohin Arewa kafafen yada labarai, wato gidajen radiyo masu wayar da kai, gargadin da ake yi na a rika nisantar juna da kuma killace kai, bai shiga kunnen jama’a ba.
8. An hana motoci shiga Kano da Kaduna, amma kuma Allah kadai ya san adadin mutanen da su ka shiga biranen biyu a ranar Alhamis da Juma’a. Shin duk lafiya garau suke tabbas? Sai an yi gwaji za a iya tabbatar wa.
9. Batun kowa ya zauna a gida ya killace kan sa bai samu karbuwa a Kano ba. Jama’a ba su kaurace daga zuwa masallatai na sallolin yau da kullum ba. Kuma maganar malaman su ta fi shiga kunnem su, fiye da gargadin Coronavirus da a ke yi musu.
10. Wakilin mu ya yo mamakin ganin yadda kasuwar garin Kura ta jihar Kano ta cika makil da jama’a, har ana tire-ture a kasuwar. Ba su damu da cunkoso ko nanike wa juna da suke yi. Kamar yadda a cikin Kano jama’a ke ta hada-hadar sayen kayan cefane har cikin dare.
Mutane sai karabkiya da hada-hadar sayen kayan cefane ake yi a cikin nishadi, kai ka ce daren jaribiri ake, gobe ta ke Sallah.
Wadannan dokokin da aka kafa, an dai killace motoci kawai, amma ba a killace jama’a, kamar yadda aka yi tunani ba.
11. Wani abin mamaki shi ne, jama’a ba su damu da ji ko sani yawan mutanen da Coromavirus ya kama ko ta kashe ba. Abin da kawai ya fi damun da yawan su, shi ne yadda za a raba kudaden da su Atiku su ka bayyana cewa sun bayar gudummawa kawai.
“Mu a raba kawai a ba kowa na sa, mu je mu sayi kayan abinc.” Inji wani mai suna Baba.
“Gwamnatin da ko takunkumin rufe baki ta kasa raba mana, ballantana maganar abinci, don me za ta ce mu zauna a gida mu killace kan mu? Su dai manyan ne ya kamata su zauna gida, su killace kan su. Dama su ne ke yawon gallafirin tsiya a kasashen Turai, har suka fiya su ka jajibo mana Coronavirus!” Inji Malam Salisu, mai sana’ar kafinta.
12. Babu abin da ya canja a Kano, musamman a yau Asabar, ko’ina cunkus, kasuwanni dankam, hatta taron daurin aure a Karkasara, bayan Asibitin AKTH, an cika makil, har ana wasa da motoci.
Discussion about this post