CORONAVIRUS: Dalilin da ya sa shugaban hukumar NCDC zai yi zaman gida na kwanaki 14 – Minista Ehanire

0

Ministan kiwon lafiya Osagie Ehanire ya bayyana cewa an umarci shugaban hukumar hana yaduwar cututtuka ta kasa (NCDC) Chikwe Ihekweazu da ya zauna a gida har na tsawon kwanaki 14 saboda ya ziyarci kasar China a kwanakinnan.

Ihekweazu wanda ya dawo daga kasar Chana ba da dadewa ba ya yi gwajin cutar Coronavirus kuma sakamakon gwajin ya nuna cewa baya dauke da cutar.

Ministan yace duk da an samu wannan tabbaci Ihekweazu zai zauna a gida na tsawon kwanaki 14 domin samun tabbacin rashin kamuwa da cutar.

Ehanire ya fadi haka ne ranar Talata a zauren majalisar dattawa da yake yi wa ‘yan majalisan bayani game da matakan kare mutanen kasa da ma’aikatar sa ta ke yi.

“Ihekweazu ya ziyarci kasar Chana ne a matsayin daya daga cikin kwararrun masana kimiya da kungiyar kiwon lafiya ta duniya (WHO) ta zaba kuma ta aika kasar domin samun bayanai game da cutar da hanyoyin da za a iya hana yaduwarta.

“Masana kimiyan da WHO ta aika sun yi kwanaki tara kuma daya daga cikin abubuwan da suka gano a kasar Chana shine mafi yawan mutanen da suka mutu a dalilin cutar na dauke ne da wasu cututtuka a jikinsu tun kafin su kama cutar.

Baya ga haka Ehnaire yace ma’aikatar kiwon lafiya ta bude wuraren gwajin cutar Coronavirus a duk tashoshin jiragen saman kasarnan da na kasa.

Ya ce an bude wadannan wurare a jihar Legas, Kano, Fatakwal da Abuja sannan a wuraren ana amfani da na’uran gwaji da zai iya gwada mutum ba tare da ya sani ba.

Daga nan sai shugaban majalisar dattawa Ahmed Lawan ya koka kan karancin wuraren gwajin cutar guda hudu da ma’aikatan kiwon lafiya ta bude a kasan.

Lawan yace kamata ya yi a bude wurare a duk jihohin kasar ko kuma a shiyoyi shida dake kasar.

Ya kuma ce zai jagoranci tawagar da za su ziyarci asibitin kula da masu fama da cutar da aka bude a asibitin Gwagwalada, ranar Laraba.

“Ina kira ga duk mutanen Najeriya da su kwantar da hankalinsu cewa gwanati na kokarin ganin Coronavirus bai yadu a kasar nan ba.

Chukwuka Utazi dake wakiltan Enugu ta Arewa daga Jam’iyyar PDP ya ce Naira miliyan 600 da gwamnati ta ware domin dakile wannan cutar ya yi kadan.

Utazi ya yi kira ga gwamnati da ta gaggauta ware wa ma’akatan kiwon lafiya Naira biliyan daya domin aikin wannan cuta.

Idan ba a manta ba a ranar 27 ga watan Fabrairu ne Ma’aikatar Lafiya ta kasa ta sanar cewa wani dan kasar Italy ya shigo Najeriya da cutar coronavirus daga kasar Italy.

Ma’aikatar ta bayyana cewa, wannan mutum dai ya shigo Najeriya ne daga kasar Italy inda bayan kwana daya da shigowa kasan ya fara rashin lafiya.

Daga nan sai aka kai shi asibiti inda aka gano cewa ya na dauke da cutar.

Babba sakataren ma’aikatar kiwon lafiya Abdulaziz Abdullahi y ace ma’aikatar kiwon lafiya ta karbi Naira miliyan 386 domin dakile yaduwar Coronavirus a kasar nan.

Abdullahi yace wadannan kudade da ma’aikatar kiwon lafiya ta karba na cikin Naira miliyan 620 da gwamnati ta ware domin hana afkowar cutar.

A yanzu haka cutar ta yadu zuwa kasashe 73 ban da kasar Chana sannan mutane 90,000 sun kamu da cutar inda daga ciki sama da 3,000 sun mutu.

Share.

game da Author