Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai yi wa ‘yan Najeriya jawabi ranar Lahadi da karfe 7 na yamma.
Hakan ya biyo bayan matsi da ‘yan Najeriya suka yi ne na ya fito yayi jawabi kamar yadda shugabannin kasashe ke yi tun da annobar coronavirus ya barke a Najeriya.
Mutanen Najeriya sun yi ta kira ga shugaba Buhari da ya yi jwabi ga ‘yan kasa ko hankalin wasu ya kwanta, domin ana ta samun bambancin ra’ayi da gaskiyar sahihancin bayyanar wannan cuta a kasar nan.
Idan ba a manta ba, ministan Yada Labarai, Lai Mohammed ya bayyana cewa shugaba Buhari zai yi jawabi a lokacin da ya fi dacewa.
Zuwa yanzu manyan jami’an gwamnati da dama sun kamu da cutar coronavirus da ya hada da shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Abba Kyari.
A ranar Asabar gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya bayyana cewa shima ya kamu da cutar, kuma ya killace kansa.
Gwamnan Bauchi, Bala Mohammed, da shugaban hukumar Imigration ta kasa Mohammed Babandede duk sun kamu da cutar.
Hukumar NCDC ta bayyana cewa Najeriya na da mutane 97 da suka kamu da cutar sannan ana gwajin wasu da dama ba a fitar da sakamakon gwajin su ba.
daya daga cikin ‘ya’yan tsohon mataimakin shugaban Kasa Atiku Abubakar ma ya kamu da cutar. Yana Asibitin Gwagwakada ana duba shi.