CORONAVIRUS: Ban yi musabaha da gwamnan Bauchi a jirgin sama ba – Atiku

0

Dan tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, Mohammed Abubakar, ya karyata kakakin gwamnan jihar Bauchi, Mukhtar Gidado, cewa da yayi wai musabaha da suka yi da gwamnan Bauchi ne ya sa ya kamu da cutar coronavirus.

A sako da ya tura wa PREMIUM TIMES ta waya, ya ce bai yi musabaha da gwamna Bala a jirgin Aero da suka shigo tare daga Legas ba.

Ya ce dukkan su suna tare da matan su ne a lokacin da suka hadu. Sannan bayan ya sauka ya wuce inda aka yi masa gwaji kai tsaye.

Sai dai kuma abinda ba a sani ba, shine gwamna Bala ya ziyarci kasar Jamus inda yayi kwanaki biyar a can. a cikin watan Maris.

Haka kuma majiya ta shaida mana cewa ” Babu abinda ya hada Atiku da gwamnan Bauchi. Sannan kuma me ya sa bai fadi cewa ya yi tafiya kasar Jamus ba sai ya bige da cewa wai musabaha yayi da dan Atiku.

Dawowar Gwamna Bala ke da wuya sai ya gana da Aliko Dangote da ministan gona, Nanono. Sannan kuma ya halarci taron bunkasa tattalin arzikin kasa a fadar shugaban kasa, inda a nan ma aka ganshi da gwamnan Edo suna tattaunawa da gwamnan Bayelsa.

Sai dai kuma har yanzu ba a san ko wadannan mutane da suka gana da gwamna Bala ko sun killace kan su ka a’a.

Share.

game da Author