Hukumar kula da tashoshin jiragen saman Najeriya ta bayyana cewa daga ranar Asabar jirgi daga kasashen waje ba zai sake sauka a Najeriya ba.
Ma’aikatar yin bincike kan cututtuka ta kasa NCDC sanar cewa an samu karin mutane 10 da suka kamu da cutar coronavirus a Najeriya.
Ma’aikatar ta ce mutum uku daga cikin suna Abuja sannan 7 a jihar Legas. Ma’aikatar ta ce dukan su sun shigo da cutar daga kasashen waje ne a ‘yan kwanakinnan banda guda daya da ya kamu ta hanyar mu’amula da mutane ne.
Yanzu an samu karin yawan wadanda suka kamu a Najeriya zuwa mutane 22 kenan.
Dukkan su na killace a na duba su.
Akalla mutane 22 ne suka kamu da cutar Coronavirus a Najeriya in da wasu 1300, suna killace ana yi musu gwaji. A jihar Katsina ma ana yin gwajin jini wani da ya dawo daga kasar Malaysia da ake zaton yana dauke da cutar
Abuja
Mahukuntan Babban Birnin Tarayya Abuja sun sanar da hana manyan tarukka da ya wuce na mutane 50 a fadin garin.
Hakan ya biyo bayan sanar da bayyanan cutar coronavirus a Abuja da gwamnati ta yi ranar Asabar.
Gwamnati ta ce dole a rage yawan muamula da juna sannan a maida hankali wajen tsaftace muhalli, da jiki.
Haka kuma Suma wuraren bauta wato masallatai da Coci-coci an umarce su day su rage yawan tara jama’a domin dakile yaduwar cutar a kasa baki daya.
Ma’aikatar yin bincike kan cututtuka ta sanar cewa an samu karin mutane 10 da suka kamu da cutar coronavirus a Najeriya.
Ma’aikatar ta ce mutum uku daga cikin suna Abuja sannan 7 a jihar Legas. Ma’aikatar ta ce dukan su sun shigo da cutar daga kasashen waje ne a ‘yan kwanakinnan banda guda daya da ya kamu ta hanyar mu’amula da mutane ne.
Yanzu an samu karin yawan wadanda suka kamu a Najeriya zuwa mutane 22 kenan.
Dukkan su na killace a na duba su.
Hanyoyi 10 da za a kiyaye domin kare kai daga CORONAVIRUS
1 – A rika Wanke hannuwa da sabulu a duk lokacin da aka dan wataya ko kuma aka yi tabe-taben abubuwa. Ko bako Kayi ka bashi dama ya wanke hannu kafin ku fara mu’amala.
2 – Ku rufe hanci da bakinku lokacin da kuke yin atishawa da gefen Hannu amma ba da tafin hannu ba. Idan kun shafi bakunan ku toh, ku wanke hannu maza-maza.
3 – A daina taba idanuwa da hannaye ko kuma hanci da baki. Ka du rika yawan shafa fuskokinku da hannaye. Idana an yi haka a gaggauta wanke hannaye.
4 – A nisanci duk wani da bashi da lafiya, musamman mai yin Mura da tari. Ko zazzabi ne yake yi a nisanta da shi sannan a bashi magani da wuri. Idan abin ya faskara a gaggauta kaishi asibiti domin a duba shi.
5 – A kula da yara sannan a rika tsaftace muhalli.
6 – A rika gaisawa da juna nesa-nesa
7 – Idan kayi bako daga kasar waje, kada a kusance shi koda dan uwana ne sai ya killace kan sa na tsawon makonni biyu.
8 – A rika Karantar da yara yadda za su kiyaye koda an aike su a waje.
9 – A yawaita cin abinci masu gina jiki, shan ruwa da motsa jiki.
10 – A yawaita yin addu’a da sadaka.
Discussion about this post